Babu Dan Kwallo A Duniya Kamar Messi ~ Inji Guardiola

Pep Guardiola kocin Manchester City ya bayyana ma duniya a wata hira da manema labarai cewa duniya bata taba samun dan kwallo ba kamar kyaftin din Argentina Lionel Messi.

A cewar BBC, Messi ya jagoranci kasarsa lashe kofin duniya na farko tun bayan 1986, bayan da Argentina ta lashe kofin duniya na Qatar 2022.

Dama kofin duniya ne ya ragema Messi kawai, a bara yaci kofin Copa America.

Messi dan shekaru 35 yaci kofinan La Liga 10 dana zakarun Turai 4 da kuma Copa Del Rey bakwai a zamansa kulub din Barcelona.

Mafi rinjayen kofunan da Messi yaci a hannun tsohon kocin sa ne Pep Guardiola wanda yayi aiki cen 2008 zuwa 2012.

A cewar Guardiola " kowa na da ra'ayinsa, amma babu mai tababar cewa shine dan wasan da duniya bata taba ganinsa ba".

Bugu da kari, Guardiola " ya kara da cewa na sha fada cewa a ganina babu kamar shi a duniya".

"Masu cewa Pele da Di Stefano da Maradona sune gwarzayensu sunyi daidai, amma a halin yanzu bayan lashe kofin duniya labarin Messi ya sake canzawa".

Messi ya kafa tarihin kasancewa gwarzon gasar kofin duniya har sau biyu a 2014 da 2022, ya dara duk yan' wasa buga wasanni a gasar da 26.

Haka kuma, ya kafa tarihin cinye kwallaye a kowane wasa tun daga rukuni har zuwa bugun wasannin karshe.



Comments

Popular posts from this blog

Civil War: Sudan's Political Turmoil and It's Solution

School problem: School Dropout In Nigerian Secondary Schools & How to Reduce It

Conflict: Science, Religion and Culture