Labarin Lafia: Yadda Cin Namijin Goro Ke Magance Cututtuka
Cin namijin goro nada matukar amfani ga lafiyar al'umma, kusan gabaki daya, namijin goro magani ne dan haka cin shi zai taimakawa lafiyar al'umma.
Kuma, namijin goro na kunshe da tarin sinadarai masu mahimmanci kamarsu "pottasium da Phosphorus" wandanda aka alakanta su da taimakawa lafiya. Bincike ya tabbatar akwai tarin "Vitamin C" da kuma Karin sinadarai da suka hada da "magnesium, calcium da zinc".
Ba lalle bane kusani, amma shekaru dayawa ana amfani da namijin goro wajen magance cututtuka kamar masu haddasa tsoro da kuma cutar da ta gagarin duniya yanzu wato ciwon sikari (diabetes).
A cewar wata mujallar " Healthline" ta jero cututtuka boyar da namijin goro ke magancewa, sun hada da:
1. Yana magance gur6acewar jini (infection): tsawon shekaru mutane da dama na amfani da namijin goro wajen magance cugwiwaka masu gurbata jini kamar su bakteriya, birus da fungi. Sannan kuma yana matukar amfani wajen magance ciwon hanta da mura.
A wani binciken 2018 ya gano cewa cin namijin goro na taimakawa wajen magance cututtukan birus, bakteriya da tari;
2. Magance kwaljewa (inflammation): cututtuka masu alaka da kwaljewa sun hada ulsa, sanyin kashi (arthritis) da sauransu. Masu dama da wadannan cututtukan na fuskantar ciwo mai tsanani a kullum. Saboda yawan sinadarin Pottasium cikin namijin goro cin shi na taimakawa wajen magance kwaljewa;
3. Magance ciwon sukari (diabetes): ciwon sukari nada wuyar sha'ani dukda cewa an cigaba wajen kimiyyar magunguna har yanzu ciwon sukari saidai a kula dashi kawai babu magani. An gano cewa cin namijin goro na rage hauhawan sukari musamman "Type 2 diabetes" mai cutar ciwon sukari akwai bukatar yawan cin namijin goro ko yaushe. Wani sinadarin "Kolaviron" bincike ya nuns yana da alaka da magance "Type 2 diabetes" da magance hypoglycemia duk da cewa binciken da akayi ga bera haryanzu ba'a gwadashi ga dan Adam ba dukda cewa sakamakon kara kwarin gwiwa.
4. Yana magance raunin garkuwar jiki (Deficient Immunity): namijin goro na kunshe da sinadarai masu yaki da cututtuka masu hana tsufa (antioxidant), yawan sinadarain dake yaki da cututtuka masu hana tsufa a cikin namijin goro na taimakawa wajen karuwar garkuwar jiki. Idan har garkuwar jiki ya karu, zai taimaka wajen hana cututtuka shiga jiki. A dalilin haka cin namijin goro kullum zai taimaka wajen karfafa garkuwar jiki.
5. Rage yawan nauyi (Overweight): saboda jiki na yawan bukatar da karancin abinci mai kone kitse (fat) da kula da lafiya, cin namijin goro sanannen abu me dake maido dandanon baki da kuma magance kishirwa. A dilin haka, cin namijin goro na taimakawa wajen rage nauyin jiki.
Comments