Hasashen Yanayi: nimet Tayi Hasashen Samun Tsananin Rana Nan Da Kwanaki Biyu
Hukumar da ke kula da hasashen yanayi a Nigeria wato "nimet" tayi hashen samun tsananin zahin rana a wasu jahohin Najeria nan da kwanaki biyu masu zuwa.
A cikin bayananta, jahohin da karuwar zahin ranar zai karu sun hada da Sokoto, Kebbi, Zamfara, Taraba, Adamawa da Oyo.
Sai kuma Babban birnin tarayya Abuja, Nasarawa, Benue, Bauchi, Gombe da Borno.
A cikin sanarwar da nimet ta fitar a ranar Lahadin da ta wuce, ta nuna zahin ranar zai karu yakai awan maki na 40°C a ma'aunin Celsius, a cikin kwanaki biyu masu zuwa.
Nimet ta kara da cewa, jahohin Sokoto, Kebbi, Zamfara, Taraba, Adamawa zahin zai wuce awon maki 40°C a ma'aunin Celsius.
Ta kara da cewa, hajojin Bauchi, Gombe da Adamawa na cikin hadari sosai saboda tsananin zafin ranar na iya shafar bangaren lahiar su.
Dan haka, hukumar ke ba mutanen jahohin shawarar shan ruwa mai yawa musamman lokuttan sahur da buda baki da kuma rage yawo cikin rana ga masu azumi.
Comments