Kiwon Kaji: Yadda Coccidiosis Ke Kashe Kaji Da Maganin Ta
Cutar Coccidiosis cuta ce dake da matukar illa ga dabbobi musamman kajin Turawa, Maja da sauransu. Wannan cutar tana cikin cututtukan "protozoa parasite" wadda tafi cutar bakteriya girma.
Kuma, Coccidiosis tana da matukar illa ga dabbobi kuma ana iya samunta a ko ina inda dan Adam ke rayuwa, karantar ta tasa dole sai anyi amfani da tubarau na ganin kananan halittu (Microscope) a ganta. Bincike ya nuna cutar takai kashi dari daban-daban, amma bai wuce kashi bakwai ke kama kaji.
Alamomin Cutar Coccidiosis Idan Ta Kama Kaji
Coccidiosis na kama hanjin kaji, tana sanyasu zawo dorowa-dorowa, wani lokaci hadda miji a cikin kashin su. Tana haddasa tsotsewar ruwan jikinsu wato (dehydration) da kuma sanya su tsamurewa da rashin nauyi (loosing weight). Idan har ba'ayi saurin daukar matakai ba kaji na iya mutuwa farat daya.
Cutar Coccidiosis na daukar sati biyu zuwa ukku kahin nuna alamar ta kama tsuntsaye. Cikin alamomin ta da za'a gani akwai kasala, takurewa waje guda kafin fara zawo. Kafin kajin da suka kamu su nuna cikakkun alamomin wannan cutar suna farawa da kashi mai ruwa-ruwa, sai zawo mai dorowa da tsanwa daga karshe kashin ko zawon na hitowa da jini musamman lokacin da takai matakin karshe.
Yadda Ake Rigakafin Coccidiosis
Galibi masu kiwo ke kai wannan cuta wajen kaji ta hanyar shiga da muamala dasu. A na iya shiga da wannan cuta ta takalmi, rigunan sanyawa da rashin tsaftace wurin zaman su da wajen abincin su da rashin wanke wuraren zuba masu ruwa.
Hanya mafi inganci ta rigakafin wannan cuta sune:
1. Kulawa da tsaftace wuraren kwanan kaji;
2. Wanke wuraren cin abincin su da ruwan shan su akalla bayan kwana biyu-biyu;
3. Masu kula da kaji su rika sanya takalma kahin shiga wajen kajin;
4. A samu riguna na musamman kahin shiga wajen kajin dan kaucewa kai masu wannan cuta;
5. Yin taka tsan-tsan wajen shige da fice da mutane a wajen kajin.
Yadda Za'a Magance Cutar Coccidiosis A Tsakanin Kaji
Hanya mafi inganci dan magance wannan cutar itace ta amfani da magungunan gargajiya. Magungunan gargajiya sun hada da:
1. Gurza ma kajin aloe vera su sha ruwanta na taimakawa sosai wajen magance wannan cutar;
2. Gurza masu Tafarnuwa cikin ruwa kajin su sha;
3. Gurza masu Turmeric cikin ruwan shan su;
4. Jika masu Tsamiya cikin ruwan shan su;
5. Gurza masu ganyen Bedi cikin ruwan shan su na matukar taimakawa;
6. A basu Albasa su ci;
Idan kajin basa shan ruwan dole ayi kokarin amfani da syringe domin dura masu jikakken maganin su sha.
Cikin magungunan wannan cuta na zamani, babba mai sauki daga cikin magungunan Turawa shine Amoxicillin, a jika masu shi cikin ruwa akalla sau ukku a rana.
Comments