Kiwon Lafiya: Maganin Rama (Lost of weight) Ga Masu Fama Da Cutar Ciwon Suga (Diabetes) Daga Abubakar Haruna
Gabatarwa Cutar ciwon suga ko a turance ana kiranta (diabetes) cuta ce dake da matukar hadari ga rayuwar al'umma wadda yanzu ta zama gagarabadau a tsakanin al'ummomin duniya baki daya. Diabetes cuta ce da a yanzu take karuwa a cikin al'umma sannan tana kisa da wuri idan ba'a dau matakin raguwar ta ba da wuri. A yanzu dai cutar bata da magani saidai a rage matsalolin da take haddasawa wato (control). Hukumar lafiya ta duniya tayi hasashen nan da 2030 masu kamuwa da wannan cutar zasu kasance yan kasa da shekaru 30 ne sabanin a yanzu ta fi yawa a wajen mutane masu dogayen shekaru kamar daga shekaru 50, 60 zuwa sama. Cutar ciwon sukari na kassara jikin dan Adam wadda a wani lokaci take sanadiyyar rasa wasu sassa na jikin mutum. Cikin alamomin wannan cuta akwai rama (lost of weight) wadda mutum ke tsanewa sosai ya koma kamar karamin yaro. Akwai bukatar masu ciwon diabetes suyi kiba amma akwai bukatar suyi zabi akan abincin da zai kara masu yawan sinadarain sukaru (calories)...