Harkokin Kudi: ISWAP Sun Rabawa Matafiya Tsofaffin Kudi A Babbar Hanyar Borno

Wasu da ake zargi yan' kungiyar ta'addanci ta ISWAP ne sun rabawa matafiya makudan tsofaffin kudi akan hanyarsu ta shigowa Maiduguri a Jihar Borno karatowar cikar lokacin canjin kudi da gwamnatin Najeriya ta sanya domin shiga masayar kudi da babban bankin Najeriya (CBN) na tsarin musayar kudi wanda ba na takardu ba (Cashless policy).

Jaridar Daily trust ta ruwaito cewa wannan lamari ya faru ne a bayan kauyen Mairari dake kan hanyar Maiduguri zuwa Monguno a ranar Asabar a karamar hukumar Guzamala dake Borno.

Wakilin Dailytrust ya kara da cewa, wadanda ake zargin na sanye da kayan sodoji (Military Camouflage) da motoci masu dauke da bindigogi biyu.

Wani mazaunin wajen, Bakura Ibrahim yace, mayakan sun daidaitu karkashin bishiya daga gefen hanya tare da manyan jikkuna shakare da tsofaffin kudi.

Ya kara da cewa, sun tambayemu cewa garin Maiduguri zamu, sai suka bamu N100,000 na tsofaffin kudi kowane daga cikin motar hayar da muke ciki. Sukace idan kuna iya zuwa banki ku canza su to kuje kuyi, Allah yasa su amfane ku.

Comments

Popular posts from this blog

Civil War: Sudan's Political Turmoil and It's Solution

School problem: School Dropout In Nigerian Secondary Schools & How to Reduce It

Conflict: Science, Religion and Culture