Yajin Aiki (Strike): Gidajen Biredi Zasu Shiga Yajin Aiki A Nigeriya
Babbar kungiyar masu biredi da abubuwan da akeyi da filawa (Association of Master Bakers & Caterers of Nigeria) zasu Shiga yajin aiki a Najeriya nan da watan Yuli.
Bayan babban taronta na masu zuwa da tsaki a ranar 22/06/2022, kungiyar ta hiddo matsalolin fake damunta kamar haka:
. Kyalewar gomnatin tarayyar Najeriya akan takardar da muke rubutama " Ministry of Trade and Investment, da ministry of finance da Central Bank of Nigeria" da rashin gamsuwa da shiga tsakanin sakataren gomnatin Najeriya;
. Karin farashin kayan aikinmu musamman filawa da sikari ya wuce hankali. Misali: yanzu buhun filawa na tsakanin N25,000 - N27,500 da kuma Karin kudin sauran kayan aiki;
. Share hiye da shekara daya da kaddamar da hukumar kula da girbin filawa ta kasa ba'a rantsar da ita ba;
. Hukumomin NAFDAC, SON, NASREA sun maidamu wajen neman kudinsu suna kakabamana biyan kudade dukda wannan lokacin na matsina tattalin arziki.
A bisa wannan dalilan, majalissar zartarwarmu ta cimma matsayar shiga yajin aiki na wakilanmu na kasa baki daya zar zuwa kananan hukumomi na tsawon sati biyu daga 13th July,2022.
Comments