Shariah: Kotu A England Zata Gurfanar da Tsohon Senator a Najeriya da Matarsa Kan Zargin Safarar Dan Adam A Yau
Wasu fitattun mutane biyu mata da miji zasu gurfana a gaban kotun Uxbridge Magistrates anjima a Burtaniya kan zargin safarar wani yaro ko yarinya da ake zaton za'a cire wani 6angare na jikinsa a Burtaniya.
Beatrice Nwanneka Ekweremadu yar' shekaru 55 da mijinta tsohon mataimakin shugaban majalissar dattawa Sen. Ike Ekweremadu dan shekaru 60 zasu gurfana a yau dan kotu ta tuhumesu da wannan ta'asa. Yanzu haka suna hannun jami'an yan'sanda na cikin binni kahin kawosu kotun.
Jaridar sky News data ruwaito wannan labari tace wasu suka tsegunta yan'sanda wannan labari sai aka tura kwararrun jami'ai na aikata manyan laihuka suka bincika suka kamasu.
Muna jiran abunda kotu zatayi ayau zuwa anjima insha Allah.
Comments