Satar Mutane (Kidnapping): Masu Satar Mutane Cikin Garin Katsina Daren Jiya

Mun samu labari jiya da dare cewa masu satar mutane (Bandit) sun shigo cikin garin katsina a wata unguwa bayan Rafin Dadi da ake kira Depree inda bayanan dake zomana sunyi awon gaba da matar wani na hannun damar Gomna Aminu Bello Masari mai suna Alh. Abdullahi Sani Gafai (Esha). Wadda aka dauka diyace ga Alh. Abdulaziz Maigoro dankwangila dake cikin garin katsina.

Bayan taimakon taimakon Allah da kokarin Jami'an tsaro an kwatota zuwa wayewar gari, wannan babban abun far in ciki ne.

Bugudakari kuma, suma wadanda aka dauka Shola qtrs satin daya wuce sauran mutum ukku da ba'a biya kudin fansarsu ba sun ku6uto.

Shawara itace dole mutane suyi duba ga yan gudun hira dake zaune cikinsu, kilan ta hannunsu ake samun bayanansu ake kawo masu wannan harin.

Sannan dole mutane suyi hadingwiwa da jami'an tsaro dan kare kansu. Zama ana kallon haka na faruwa ba tare da daukar mataki ba zai zamo abun alkhairi ba.

Allah ya kiyaye gaba, ya kawo mana zaman lahia

Comments

Popular posts from this blog

Civil War: Sudan's Political Turmoil and It's Solution

School problem: School Dropout In Nigerian Secondary Schools & How to Reduce It

Conflict: Science, Religion and Culture