Hutun Karshen Zango: Abubuwan Da Ya Kamata Yara Suyi Lokacin Hutu Maimakon Zaman Banza

Lokacin hutu lokaci ne da yara ke barin zuwa makaranta zaman gida ya karu. Wannan karon yara sun Shiga hutun karshen zangon karatu a Najeriya inda yara zasu samu Karin lokutta basa yin komi. Makarantun firamare da sakandare sun Shiga dogon hutun da zai kaisu zaman sati biyar zuwa shidda a gida babu zuwa makaranta. 

A wata hira da BBC Hausa tayi da wani mai makaranta mai zaman kanta a Abuja Najeriya Alh. Muhammad, da kuma karin haske da nayi. Alh. Muhammad yayi karin hasken abunda ya kamata iyaye da yaransu suyi a wannan lokaci na hutun karshen zangon karatu. Shawarwarin da ya bada sun hada da:

1. Amfani da Manhajar koyon karatu (Software): ana amfani da ita domin koyon karatu da kanka kai tsaye. Manhajojin sun hada da "You lesson", "Mimo (coding)" da sauransu. Ana bukatar iyaye suyi rijista sannan suna zaune da yaransu suna kula da yadda suke koyon karatun kai tsaye.

2. Akwai abubuwan da basu shafi karatu ba kamar su wasannin kamar su langa, carafke, kwallon kafa, kwallon kwando, kwallon hannu, wasan buya, ziyarar wuraren shakatawa, wasannin hawan doki, dambe, kokowa da ninkaya.

3. Aikin gida: musamman ga diya mace, lokacin hutu zai zama wata damace ga iyaye su koyawa yaransu mata dubarun kulawa da gida wanda suka hada da girke girke, wanke wanke, wankin kaya, gyaran dakuna, goge goge da sauransu.

4. Amfani da mutum mutumi: akwai mutum mutumin yara ke iya amfani dashi domin koyon karatu. Idan iyaye nada karfin samar dashi suna iya sawowa yaransu don koyon karatu. Mutum mutumi shi ake kira da suna "Robot" a turance.

5. Yin karatun litattafai: ga yara da iyaye masu son karatun litattafai lokacin hutu wata dama ce suke iya amfani da ita domin koyon karatun litattafai masu yawa. Haka yaranka zasu goge wajen karatun da sauri sosai.

6. Karin karatwasu "Extra lesson ": iyaye na iya samar da wani ko wata malami ko malama dan koyar da yaransu karin karatu domin samun hazaka sosai na wasu darassu masu mahimmanci. Extra lesson na taimakawa matuka wajen gane darussa masu mahimmanci garesu.

7. Koyon sabbin harsuna: iyaye na iya amfani da wannan damar dan koyawa yara harsuna sosai musamman masu mahimmanci ga zamantakewar rayuwarsu.

8. Kallon fina-finai masu amfani: iyaye na iya amfani da wannan lokaci domin samawa yaransu fina-finai masu koya abubuwa a rayuwa sosai kamar na koyon girke - girke ga mata, kere - kere ga maza da mata, dubarun yaki, dubarun kare lahia a matakin farko da sauransu.


Comments

Popular posts from this blog

Civil War: Sudan's Political Turmoil and It's Solution

School problem: School Dropout In Nigerian Secondary Schools & How to Reduce It

Conflict: Science, Religion and Culture