Shawarwarin Tsaro (Security Advises): Shawarwari 15 Da Hukamar Yan' Sandan Najeriya Suka Bayar Don Kare Kai

Babban sufeton yan' sandan Najeriya Usman Alkali Baba a wata sanarwa da ya fitar 14th Agusta, 2022 kan yanayin tsaro a Najeriya ya bayar da ummarnin matakan kare kai ga yan Najeriya baki daya.

Sannan shugaban ya kuma umarci jami'an da su rika gudanar da sintiri da bincike akai-akai dominated rage aikata many an laifuka a kasar.

Kuma hukumar ta roki yan Najeriya da suyi hakuri da sauye-sauyen da zasu gani saboda zasu rika ganin jami'anta wurare daban-daban suna tsayar da mutane domin bincike.

A saboda hakane hukumar ta fitar da matakan kare kai ga yan kasar guda 15 Lamar haka:

1. Kada Ku manna wata alama da zata nuns aikinku ko wurin da kuke aiki, musamman idan inda kuke aiki babba ne.

2. Kada kusa hotunan ya'yan'ku sanye da kayan makarantarsu ko bajen makarantarsu a shafikan intanet.

3. Idan kunje wajen taron Niki  kada Ku rika lika kudi, a maimakon haka ku sanya kudin cikin ambulam Ku ba makadan kai tsaye.

4. Kada kuje ATM cirar kudi masu yawa ko ku nemi karar da kudin dake ciki. Ba sai kasa Naira dubu 50 a jikkar ka ta aljihu zai nuna kai mai kudi ne.

5. A koyaushe ka rika goge sakonnin da bankinka ke turo maka ta waya na hada-hadarka. Zaka iya haddace bayannan yawan kudin da suka rage maka a asusunka ba sai ka bari  wayarka ba. Ka yage lasisin POS ko ATM ka jefar.

6. Kada kubi wajen da keda duhu ko ba mutane sosai lokacin da kuke motsa jiki. In ya zama dole kuyi, ku kasance tare da wadanda kuka yarda dasu.

7. Ko yaushe Ku tabbatar da kun rufe kofarku ko da zaki fita ne kawai. Ku kashe janaretocinku.

8. Kada ku rataya katin wajen aikin ku idan ka FIFA saga wajen aiki. Babu mai bukatar sanin wajen aikinku.

9. Ku rika sanar da iyalanku ko iyayenku inda kuke ko yaushe.

10. Kada Ku aiki ya'yan'ku su kadai waje. Ku tabbatar kun hadasu da wani babba.

11. Kada Ku nuna kanku cewa ku many an mutane me ko masu kudi ko a unguwarku, kuna rabon kudi ko wasu abubuwa.

12. Ku rika yin komi cikin sirri yafi.

13. Kada Ku rika dadewa wajen aiki bayan an tashi har zuwa dare. Kuna iya Baron sauran aikin zuwa washe gari.

14. Kullum Ku rika kawo matakan kariya ko yadsa zaku kaucewa Shiva matsala a duk abunda zakuyi ko zakuje.

15. Kusan irin abubuwan da zaku rika sanyawa game daku a shafikan intanet.

Comments

Popular posts from this blog

Civil War: Sudan's Political Turmoil and It's Solution

School problem: School Dropout In Nigerian Secondary Schools & How to Reduce It

Conflict: Science, Religion and Culture