Matakan Tattalin Arziki: Dubarun Rage Cin "Data" Don Shiga Intanet
A yanzu data nada matukar amfani ga rayuwar al'ummar duniya baki daya saboda masayar bayanai. Mahimmancin data a yanzu ya kusa daya dana abinci da kudin kashewa. Amfani da data bai tsaya kan samari da yan'mata ba, kawao harda manyan mutane saboda shiga dan sanin halin da duniya take ciki.
Duk duniya anti itifakin Najeriya na daya daga cikin kasashr masu tsadar data, wasu kasashen data kyautane da zaran ka sayi katin buga waya za'a bada data kyauta.
Yan' Najeriya sunyi koke-kore kala-kala dan rage farashints amma abun yaci tura.
Kamfanonin wayar na koken cewa rashin wutar lantarki da tsadar diesel na sanya sana'ar tasu cikin gararin tsada, shiyasa farashin data da kira ways ya gagara raguwa a kasar.
Duk da haka mutum na iya amfani da dubaru dan rage banna da asarar data lokacin shiga yanar gizo ta intanet. Dubarun sun hada da :
1. Iyakance yawan "Data" da manhajojji waya zasuyi amfani dasu wanda a turance ake cewa "data limit". Wannan na daga cikin hanya mai sauki dan hana manhajoji da ba'a bukatar su ci data.
2. Idan za'a sabunta manhajojjin waya (update) ayi amfani da Wi-Fi. Ana samun Wi-Fi a babban wuri ko ofishin da ake aiki da ake samar da ita da harha da kuma sauki.
Akwai bukata a shiga waya dan kashe " automatic update".
3. Ku tabbatar wayarku bata tare da "malware": malware wata manhajace da aka kera dan lalata wayoyi, samun Samar samun bayan mutum ba akan ka'ida ba. Malware ba kawai tsotse ma mutum data sukeyi kadai ba harda tana iya haddasa ma mutum rasa muhumman bayanai a waya ko komfuta.
4. Kashe manhajar " Google map" : idan har manhajar Google map na kunne kai tsaye ba tare da tare da bata ummarni ba wata cigaba da aiki, kuma aikin nata na cin datar da ta wuce kima. Yadda mutum zaiyi shine a maida ta "offline".
Comments