Matsalolin Haihuwa: Mi ke Kawo Kan Yara Girma?

Abubuwa da yawa ke kawo girman kokon kan yara girma, wanda kuma kan janyo ma yaran da iyayensu damuwa sosai. Damuwar ta hada da munin fuskar yaran da nakasa da ciwace-ciwace da ka iya shafarsu.

Abubuwan Dake Kawo Wannan Matsala

1. Taruwar gur6ataccen dorowa, ko tsanwar ruwa na matattun kwayoyin jini farare (white blood cells) da bakteriya da ake kira a turance "cerebral Abscess". Taruwar ruwan sosai na taimakawa wajen karuwar girman kokuwar kan yara.

2. Karuwar yawan kwalwa wanda shima a turance ake kira da suna " tumour cerebri". Kari ne dake fitowa a cikin kwalwa, ana ganeshi  ta hanyar wadannan alamomin kamar  su yawan ciwon kai, makanta ko gani sama-sama da wani lokaci ana fita hayaci.

3. Taruwar ruwa cikin kai : wanda shima a turance ake kira da  "Hydrocephalus". Abubuwan dake sanya taruwar ruwan sun kunshi ciwon fashewar jijiyar kai, sankarau, buguwar kai da sauransu. Alamomin da ake gane taruwar ruwan sun hada da amai, ciwon kai mai tsanani da kumburin idanu.

4. Sankarau ko " meningitis" a turance na daya cikin cututtukan dake kawo German kokuwar kai, cikin alamomin gane sankarau sun hada da zazzabi mai tsanani, ciwon kai mai tsanani, ciwon wuya ko makewar wuya da kin son zama cikin haske.

5. Taruwar jini : taruwar jini a cikin kwalwa na kara taimakawa mutum wajen karin girman kokuwar kai, hakan na faruwane saboda buguwa a kai ko kuma hatsarin ya kawo buguwar kokuwar kai.

6. Gado : wasu nada gadon girman kokuwar kai : akwai cututtuka masu yawa dake haddasa kan jariri girma fiye da kima. Dangin cututtukan sun hada sturge weber syndrome, neurofibromatosis da sauransu.

Yadda Za'a Magance Wannan Matsala

Ya danganta da mi ya kawo wannan cuta, ziyartar asibiti ganin likita shine matakin farko. Likitocin kanyi tiyata idan akwai bukatar hakan, likitan wannan aiki ana kiranshi da suna "neurosurgeon".

Akwai gwaje gwaje da ake bukata kahin yin wannan tiyatar. Gwaje gwajen sun hada da computed tomography (CT Scan), molecular genetic, CSF analysis da Head Ultrasound scan wanda ake kahin madigar jariri ta rufe.

Akwai kuma kwayoyin magunguna idan an samu jijjiga ko farfadiya. Magungunan sun hada da acetazolamide, Mannitol da sauransu.

Akwai kuma tiyata da akanyi idan bukatar hakan ta samu domin zuke ruwan daya taru. Hanyoyin sun hada da ventricular peritoneal shunt da ventricular -cisternal shunt.


Comments

Popular posts from this blog

Civil War: Sudan's Political Turmoil and It's Solution

School problem: School Dropout In Nigerian Secondary Schools & How to Reduce It

Conflict: Science, Religion and Culture