Kayan Marmari: Amfanin Abarba Ga Lafiyar Mutum
Kayan marmari, kayane da ake ci dan jin dadi da Gina jiki. Bayan haka likitoci na bada shawarar cin su da amfani dashi domin kiyaye lafiyar jiki.
Kayan marmari sun hada da su ayaba, lemun zaki, kankana, abarba, attufah da sauransu.
A nan zamuyi magana akan yadda cin abarba ke kara gina jikin dan Adam.
Amfanin Abarba Wajen Gina Jikin Dan Adam
1. Rana bada Mariya daga cututtuka : watau tana dauke da sinadaran "antioxidant" wanda ke taimkawa wajen rage kamuwa da cututtukan kansa, sukari da zuciya.
2. Tana karawa jiki garkuwa : tana matukar taimakawa wajen karfafa garkuwar jikin dan Adam ta hangar kare jiki daga kamuwa daga cututtuka sosai.
3. Tana dauke da sinadarai masu gina jikin dan Adam: Abarba na dauke da sinadarai masu yawa masu kara lafiyar jikin dan Adam kamar su "copper, vitamin c, vitamin B6, manganese, fiber, protein, calories,carbs, thiamine, folate da pottasium". Wanda dukansu ke taimakawa jiki da kaifin kwalwa.
4. Tana taimakawa wajen saurin narkar da abincika: akwai bukatar bayan ancient abinci ya narke da wuri. Yana daga cikin aikin Abarba narkar da abinci da wuri dan jiki ya samu saukin amfani dashi da wuri.
5. Tana taimakawa wajen magance ciwon gabobi da ciwon baya: Abarba na taimakawa wajen rage ciwo da radadin ciwon gabobi da kumburin gabobi (Arithristis) da ciwon jiki. Tana kuma rage radadi ciwon baya bayan anyima mutum tiyata.
6. Rage kitse da te6a : tana taimakawa wajen rage kitse da ke jikin dan Adam sosai muddun ana shanta akai akai.
7. Tana taimakawa lafiyar kashi da Samar da haihuwa da wuri : bincike ya nuna shan abarba na taimakawa lafiyar kashin dan adam da gina shi da kuma taimakawa wajen samun haihuwa da wuri.
Comments