Rashin Gyaran Jiki: Mi ke Kawo Zubewar Kyan Jikin Mace Bayan Aure?

Dan kinyi aure baya nufin shikenan kin gama ko kin tsufa, sai a daina gayu da kwalisa, yin haka ba daidai bane. Ko da kinyi aure kin haihu baya hanaki gyaran jiki da kyautata jikin ta hanyar kwalliya da gayu ga mijinki, yin haka zai sa ki kara daraja a wajen miji.

Galibin mata sun dauka cewa kwalliya da gyaran jiki na yan mata ne ko anayi ne lokacin mace na budurwa ko tana neman mijin aure ko mashinshini. Rashin kwalliya da gyara jiki ga mata masu aure ya jawowa mafi yawa daga cikinsu matsala. Matsalar ta hada da rashin kula daga miji da kuma yan kalle kallen matan wajen masu kwalisa. Yar'uwa kiyi bakin kokarinki wajen gyaran jikinki da tsafta dan hana mijinki kallon mata a waje ko tunanin yi maki kishiya babu shiri. 

Cikin gyararrakin da zakiyi sun hada da:

1. Gyaran nono dan kada ya fadi da diri;

2. Gyaran fatan jiki tayi kyalli;

3. Yin kwalliya dan miji ya gani;

4. Yin kwalliyar tufafi

5. Sanya turare a jiki ko yaushe dan miji yaji kanshi.

Dalilan Zubewar Kyan Jikin Mace Bayan Aure

Ga wasu daga cikin dalilan da mukayi azari a kansu:

1. Rashin bada Tazarar haihuwa : jahilcin ma'aurata akan hali ko lokacin da mace ya kamata ta dau ciki, na daga cikin abunda ke jefa mata rama da zubewar tsayuwar nonon da diri. Shiyasa da yawa daga cikin su suke yin gwammai lokacin da suke goyo. Damuwar kula da yara da shan nono da yi masu wanka da sauransu na cikin manyan abubuwan da ke jefa su halin damuwa daga nan sai zubewar duk wani abun kyau daga jikin mace. Bada tazarar haihuwa na taimakwa mace wajen maido abubuwan da ta rasa lokacin haihuwa da lokacin goyon da ko diya.

2. Rashin bada Abinci Mai gina jiki : tabbas cin ABINCI mai kyau da inganci na taimakawa jikin mace Yayi kyau matuka. Idan mace bata samun ingantaccen ABINCI mai kyau da gina jiki, kyau da martabar jikin ta zasu zube.

3. Rashin Zaman Lahia a gidan aure: akwai mata da yawa dake fama da rashin hankali gidan sure ko dai tsakaninta da miji ko kishiya ko uwar miji ko dangin miji ko makwafta. Shiga wannan damuwar na haifarwa mace shiga matukar damuwa da ka iya kaita ga rama da rasa duk wata sura mai kyau a jikin ta.

4. Yawan Jima'i daya wuce kima: dayawan mutane sun dauka cewa yin jima'i kullum shine abunda ake bukata, amma yinshi kullum na iya haddasa matsalolin ga jikin mata da miji. Yin jima'i daya wuce kima na haddasa damuwa musamman ga mata. Akwai maza masu shaye-shayen magungunan karhin maza da ke sanyasu jima'i na tsawon lokaci har sau goma a rana, hakan ke haddasa matukar damuwa ga mace daga nan sai rama da zubewar kyan jiki saboda shan murza ko yaushe.

5. Shaye-shayen kwayoyi da magunguna ba tare da ummarnin likita : akwai daga cikin mata da suka fada dabiar shaye-shaye wadda hakan ke kawoma jiki matukar damuwa. Muddun jiki na ta'amulli da kwayoyin wannan jikin zai lalace gaba daya.

Yadda Zaki Gyara Kyan Jikinki

1. Akwai bukatar ki rika bada tazarar haihuwa dan samun hutu kahin kara wata haihuwar, akalla shekaru biyu tsakani ko sama da haka, gwargwadon fahimtarki keda mijinki.

2. A tabbatar miji na samar da ABINCI mai gina jiki da kayan kwalliya kala-kala.

3. Dole a kaucewa ko wane iron tashin hankali a gidan aure.

4. A rika yin jima'i gwargwadon kima kamar sau ukku ko hudu a sati, sannan a kaucewa shan magungunan karhin maza masu hatsari.

5. Dole ne mace ta kaucewa shaye-shayen magunguna kowane iri imba da ummarni likita ba.

Idan har aka bi wadannan shawarwari insha Allah mace zata cigaba da zama dumul-mul tare da birge mijinta na aure.


Comments

Popular posts from this blog

Civil War: Sudan's Political Turmoil and It's Solution

School problem: School Dropout In Nigerian Secondary Schools & How to Reduce It

Conflict: Science, Religion and Culture