Posts

Showing posts from April, 2023

Civil War: Sudan's Political Turmoil and It's Solution

The Islamic Republic of Sudan, one of the Northeast African country that has been  experiencing decades of political turmoil, conflict, and civil war. The Sudan's complex history is marked by political instability, ethnic, religious crisis and economic challenges. In history, one of the most significant things in Sudan's conflicts and civil wars were the 2nd Sudanese Civil War, which lasted 22 years from 1983 to 2005. This war was fought between the coaliation of Sudanese government, led by the Arab-dominated National Islamic Front, and various rebel groups, including the Sudan People's Liberation Army/Movement (SPLA/M), the represented marginalised groups in the south of the country, who sought greater political representation and independence. The conflict was characterised by brutal violence, consists widespread human rights abuses, displacement of millions of people mostly women and children and famine. It is estimated that over two million people lost their lives in th...

Kidaya (Census): Gaskiyar Magana Akan Dalilan Dage Training Na Supervisors Da Enumerators A Kidayar 2023

Jaridar Punch ta 22th April, 2023 ta ruwaito cewa gwamnatin Nigeria ta dade ta na kakarin sake sabuwar Kidaya (census) bayan wadda akayi a 2006 a kasar saboda mahimmancin ta. A baya gwamnati tayi yunkurin yin kadaya (census) tun 2016 kamar yadda majalissar dinkin duniya (United Nations Charter) ta tanada amma haka bata cimma ruwa ba. A baya-bayan nan gwamantin Muhammadu Buhari ta yanke shawarar yin wannan kidaya (census) a shekarar 2022, amma halin tattalin arzikin kasar ya sanya an dage yin wannan gagarumin aikin zuwa shekarar 2023 bayan babban zaben kasar. Kuma, kusan hukumar National Population Commission (NPC) ta shirya tsaf don yin wannan aikin a shekarar 2023, har ta dauki ma'aikatan wucin gadi da koyawa wasu daga ciki aiki da biyansu kudin training, saidai shima wannan yunkurin ya fara fuskantar kalubale jim kadan da fara shirin koyon aiki (Training) ga Supervisors da Enumerators. NPC ta gama shiri da fidda sunaye a kowace karamar hukuma da zabar makarantu da za'ai wanna...

Aure (Marriage): Lokacin Da Yafi Dacewa Mace Tayi Aure Da Fara Haihuwa A Kimiyyance

Yin aure da fara haihuwar yara wasu shawarwari masu girma, na da mahimmanci kafin yin aure da fara haihuwa, mutum ya tabbatar an shirya. Amma wane lokaci ne wanda yafi dacewa mata suyi aure da haihuwa? A kimiyyance, akwai wasu abubuwa da ya kamata a kula. Bincike ya nuna mata da suka jira har sai karshe shekarun su na Ashiri (late 20s) ko farkon shekarun su na Talatin (late 30s) sun fi samun damar zaman lafiyar aure akan wadanda akayiwa aure da kananan shekaru (early 20s) saboda mutane wadanda suka makara wajen aure sau dayawa sun fi natsuwa da hankali, sannan suna iya jurewa kalubalen aure dake tasowa.  Wajen haihuwa kuma, shekaru da suka fi dacewa mace ta haihuwa yana tsakanin shekaru 20 da 35. Mata a wannan lokacin sun fi samun lafiyayyen daukar ciki (healthy pregnancies) da samun lafiyayyun yara (healthy babies). Mata wadanda suka jira har zuwa karshen shekara 30 (late 30s) ko karshen shekaru 40 (late 40s) su haihuwa sun fi samun matsalolin haihuwa wajen daukar ciki da haihuwa ...

Rigakafin (Malaria Vaccine): Za'a Fara Rigakafin Malaria A Nigeria

Bayanai daga mujallar Health wanda Same Emmanuel ya ruwaito cewa, hukumar dake bada amincewar magunguna a Nigeria wato "National Agency for Food and Drugs Administration and Control (NAFDAC) ta amince da sabon rigakafin R21 Malaria vaccine wanda kamfanin Serum Institute of India ya kirkiro. Shugaban NAFDAC (Director General) Prof; Mojisola Adeyeye ya fadi haka ranar Litinin 17th April, 2023 a Abuja. A wannan dalili ne ake cewa Nigeria ta zamu ta biyu bayan kasar Ghana da ta amince da wamnan sabon rigakafin da aka kirkiro a jami'ar Oxford. Prof. Adeyeye yace maganin zai iya magance cutar malaria ta kananan yara daga dan wata biyar zuwa wata 36 da haihuwa. Nigeria na jiran akalla kwayoyin ragakafi 100,000 kyauta (Donation) bada dadewa kafin ya shiga kasuwa sannan za'ayi shiri da hukumar lafiya a matakin farko wato National Primary Health care Development Agency (NPHCDA) dan fara aiwatar da ita. Adeyeye ya kara da cewa, NAFDAC wajen gudanar da aikin ta akan doka ta amince da ...

Ganin Watan Shawwal (1444): Yaushe Ne Ranar Sallah, Alhamis ko Juma'ah?

Bayanai da kamfanin jaridar Saudi Gazette ya bayar, yace bincike na kimiyya ya nuna da wuya aga jinjirin watan Shawwal ranar Alhamis 20/04/2023 wanda yayi daidai da 29/09/1444 a kasashen Larabawa da sauran sassan duniya. A cewar shugaban hukumar dake kula da wannan bincike Engr. Majed Abu Zahra yace rana zata riga wata faduwa a inda rana a Makkah zata fadi a 06:42 pm, wata zai kasance saman rana da tsawon 04 degrees, sannan karkatawar wata (elongation angle) daya raba wata daga rana shi kuma ya kai (05 degrees) da kuma hasken wata wato (illumination is 0.2%). Bugu da kari, wata kuma zai fadi (Moon Set at 7:06pm) bayan Minti 24 da faduwar rana, a lokacin ne sharadin shiga jinjirin watan Shawwal (Condition for entering month of Shawwal will be fulfilled Astronomically) zai cika. Abu Zahra ya kara da cewa, ganin jinjirin watan Shawwal (Shawwal Crescent) kuru-kuru ko ta amfani da na'ura (Mornitoring device) ba zai yiwuba sai ta hanya kamera ta musammanr (CCD Camera) saboda karancin has...

Magani (Medicine): Sirrin Dake Cikin Tafarnuwa Wajen Magance Ciwon Sankara

Dayawan mutane sun yarda cewa Tafarnuwa (Garlic) na da karfin yakar cutar sankara (cancer) saboda sabon bincike na kimiyya da ya tabbatar da cewa tana yakar wasu daga cikin ciwukan sankara (cancer). Mafiyawa kuma sun aminta da wani binciken dake cewa cin Tafarnuwa (Garlic) na da alaka da rage yaduwar wasu ire-iren cutukan sankara (cancer) kamar su ta ciki (Stomach cancer), kwankwaso (colon cancer), mafitsara (prostate cancer) da ta nono (Breast cancer). Sinadarin "fibre" dake cikin Tafarnuwa (Garlic) a taimakawa wajen hana yaduwar mafarar sankara (Tumour) da sauran amfanuka. Bugu da kari, saboda kasantuwar ta na zama maganin sankara (cancer), Tafarnuwa (Garlic) nada wasu amfanuka ga lafiya kamar su: rage kwajewa (anti-inflammation), rage bargo ( anti cholesterol) da karin karfin dakarun jiki (improve immune system). Kuma, yana da mahimmanci cin Tafarnuwa (Garlic) a cikin abinci, duk da haka bai nuna a rika cin ta ba tsari. Amfanukan Tafarnuwa sun hada da:  1. Yakar kwayoyin c...

Azumi (Fasting): Muhimmancin Azumi Ga Lafiyar Yan' Adam

Idan aka cire wajibcin azumi ga musulmai a lokacin watan azumin Ramadan mai daraja, azumi kanshi nada amfani marar misali ga lafiyar mutane. Daga rage kiba zuwa samar da lafiyayyen jini zuwa ga lafiyar zuciya da kuma lafiyar hanyoyin jini, azumi (fasting) ya zama hanya mafi sauki wajen samar da lafiya da hana tsufa da wuri (anti-aging). Duk da cewa, ba kowa yasan alfanun da azumi yake kawowa jikin dan Adam ba, a nan zamu tsakuro wasu daga cikin su kamar haka: 1. Cire gurbatattun abubuwa daga jiki (Detoxification): rashin cin abinci na lokaci mai tsawo babbar hanya ce ta wanke jiki daga cututtuka da cin abinci ke kawo su (detoxification), kara lafiyar sassan jiki (body organ), wanke bangarorin jiki dake dagargaza abinci (digestive system), habbaka zagayawar jini (blood circulation) da wanke duk wata cuta dake iya cutar da jiki (toxins); 2. Yana maido da son cin abinci da abun sha ( Improve Appetite): tsawon lokaci da ake shafewa ana cin abinci na haifar da matsalar rashin son cin abinci...

Magani (Traditional Medicine): Tumfafiya da Alfanun Ta Ga Lafiyar Al'umma

Itaciyar Tumfafiya (Calotropis Procera) na da dogon tarihi wajen magance cututtuka (diseases) a cikin al'ummomin duniya baki daya. Muhimmancin ta wajen magance matsalolin rashin lafiya yasa masu magungunan gargajiya (Herbalists) basa son mutane na zuwa inda take dan kada su gano magungunan da take su hana su samun kasuwar magunguna. Kuma, a haka aka rika tsorata mutane akan wannan itaciyar da cewa tana mu'amala da Aljannu (Evil Spirits) tana biyo mutane a gida da sauran su. Amma a cikin wannan bayanai zaku karanta yadda take amfanar da lafiyar jikin mutum a fagage daban-daban kamar haka: 1. Furen Tumfafiya na maganin mayu matukar gaske. Duk mai cin furen ta maye bayason irin ruhun su, dan haka mutum ya kubuta daga sharrin su; 2. Ana amfani da ita wajen maganin cizon macizai (anti-snake bite). Anan saiwar ta ce babban mahadi dan maganin cizon macizai. Sai a tuntubi masana dan sanin yadda za'ai hadin a koya; 3. Idan aka turara bawon ta aka hadashi da garin Habbatissaudah  kow...

Social Inequality: The System of Social Inequality In Nigeria

Social inequality refers to the unjust distribution of resources, opportunities, and privileges among societies or groups in a society. It is a pervasive and has a long historical problem in many societies around the world, and it roots can be traced back to different factors including  historical, political, economic, and cultural. The earliest theories of social inequality was developed by Karl Marx and Friedrich Engels in the 19th century. They both argued that the capitalist system, in which the means of production are own by privates and operated for huge  profit making, creates a class system where the bourgeoisie (the owners of capital) exploits the proletariat or labourers for their labours. This resulted in a widening wealth gap between the two: poor and rich which perpetuates social inequality or social injustice. However, another influential theory that also explaines social inequality is structural-functionalism, developed in 20th century by Emile Durkheim. Based o...

Kayyade Iyali (Family Planning): Yadda Zakuyi Amfani Da Aloe Vera Dan Kacewa Daukar Ciki

Wani bincike na kimiyya da aka wallafa a jaridar Telegraph 2017 ya bada haske ga milliyoyin mata a duniya dake neman magungunan hana daukar ciki (Contraceptive pills) ba tare da bi baya ba (Side effect). Haka, kamar yadda editan jaridar ta rubuto wato Sarah Knapton tace wani sinadari (Chemical) da aka samu a cikin Aloe Vera da Thunder god Vine (babu sunan shi da Hausa) ya samar da haske wajen samun wannan maganin marar illa. Sinadaran da wannan tsirrai ke fitarwa na iya samar da maganin wanda bai bukatar sinadaran hormone a ciki ko kuma "molecular condom" wanda ake sha kafin ko bayan jima'i (before & after pills). A wajen al'adun magungunan gargajiya wato " Folk Medicine tradition" sinadaran aloe vera da thunder god vine dukansu an ruwaito suna kawar da ciki da ba'a bukata (unwanted pregnancy) da kuma samar da abubuwa masu amfanar jiki. Bugu da kari, masana kimiyya (Scientists) sun fiddo sinadarai biyu "Lupeol" daga aloe vera da "Prist...

Kidaya (Census): Jadawalin Biyan Ma'aikatan Wucin Gadi Na Census 2023

Hukumar kidaya ta kasa wato National Population Commission (NPC) ta fitar da jadawalin biyan ma'aikatan wucin gadin kidaya ta kasa a kidayar 2023. A cewar NPC, ta raba tsarin biyan kudin zuwa gida biyu, wato alawus (allowance) da kudin aikin (Basic Salary). Evelyn Arinola Olanipekun, director census department tace ma'aikatan wucin gadi zasu karbi alawus kala ukku: kudin abinci, kudin zirga-zirga da kudin training. A karkashin alawus na abinci, ma'aikatan wucin gadi zasu karbi alawus biyu: specialised workforce (SWF) da state facilitators. A cewar jaridar Punch, SWF zasu karbi N26,000 a cikin kwanaki ukku tare da kudin training na jaha cikin kwanaki 10 daban, sai kuma facilitators zasu karbi N26,000 a cikin kwanaki 10. Kudin abun hawa (transport allowance) na duk ma'aikatan wucin gadi N20,000. Trainers allowance kuma za'a biyasu N15,000 a kowace rana cikin kwanaki 13 da  kwanaki 10 na state facilitators amma kudin training kuma N10,000 a kullum cikin kwanakin traini...

Kidaya (Census): An Sanya Sabon Lokacin Yin Training Na Supervisors da Enumerators A Census 2023

A baya sanarwa ta nuna cewa 31st March, 2023 hukumar National Population Commission (NPC) zata fara training jami'anta na wucin gadi wato adhoc staffs, yanzu an samu sauyin lokaci saboda wasu abubuwa masu mahimmanci da suka taso. Bayan wani taron karawa juna ilimi (Workshop) a kan census na 2023 wanda ya gudana a Golden Tulib Hotel na Port-Harcourt dake jihar Rivers, jami'an NPC sun amince da sabbin ranaku na training din supervisors da enumerators. NPC tace, ta canza ranakun training daga 31st March, 2023 zuwa 11th April, 2023 a gama 17th April, 2023. Wannan ne kashi na farkon training na supervisors da enumerators. Sannan LGA level Training on Persons' enumerators zai fara a 25th April, 2023 ya kare 29th April, 2023. Wannan ne kashi na biyu na training din supervisors da enumerators. Census Night kuma zai wakana a 2nd May, 2023, sannan census din zai wakana ne a tsakanin 3rd May, 2023 zuwa 7th May, 2023. Bugu da kari, wannan sanarwa an bada ta ne a lokacin taron masu ruwa...