Kidaya (Census): Gaskiyar Magana Akan Dalilan Dage Training Na Supervisors Da Enumerators A Kidayar 2023
Jaridar Punch ta 22th April, 2023 ta ruwaito cewa gwamnatin Nigeria ta dade ta na kakarin sake sabuwar Kidaya (census) bayan wadda akayi a 2006 a kasar saboda mahimmancin ta. A baya gwamnati tayi yunkurin yin kadaya (census) tun 2016 kamar yadda majalissar dinkin duniya (United Nations Charter) ta tanada amma haka bata cimma ruwa ba.
A baya-bayan nan gwamantin Muhammadu Buhari ta yanke shawarar yin wannan kidaya (census) a shekarar 2022, amma halin tattalin arzikin kasar ya sanya an dage yin wannan gagarumin aikin zuwa shekarar 2023 bayan babban zaben kasar.
Kuma, kusan hukumar National Population Commission (NPC) ta shirya tsaf don yin wannan aikin a shekarar 2023, har ta dauki ma'aikatan wucin gadi da koyawa wasu daga ciki aiki da biyansu kudin training, saidai shima wannan yunkurin ya fara fuskantar kalubale jim kadan da fara shirin koyon aiki (Training) ga Supervisors da Enumerators.
NPC ta gama shiri da fidda sunaye a kowace karamar hukuma da zabar makarantu da za'ai wannan training, saidai kasa da awa 24 da fara wannan aiki aka bada sanarwar dage wannan aiki har sai baba ta gani (Indefinite postponement).
Wani bidiyo da ya rika yawo bayan wannan dage wannan training ya nuna wani jami'in hukumar NPC Controller na karamar hukumar Chanchaga Mal. Sanusi Maigida, yana shedawa wani taron matasa cewa an dage wannan aiki ne saboda anyi kutse (hacking) ga manhajar hukumar. Saidai daga baya hukumar ta karyata shi kuma tace babu wani kutse (kutse) ga manhajar ta saboda tayi shiri na musamman domin bata kariya. Sannan tace, hukumar zata hukunta shi saboda kunyatar da ita da yayi a idon duniya.
Bugu da kari, babban abunda yasa aka dage shirin koyon aiki (training) na supervisors da Enumerators rashin kudi ne. Kudin da ake bukata dan wannan aiki yakai N626bn, idan an hada harda ayyukan bayan kidaya (census) sun kai N868bn. Abunda gwamnati ta bada kashi 45% cikin dari ne wanda sun kai N291.5bn saura cikon N327.2bn.
Saboda wannan matsalar ta kudi da take damun hukumar yasa ake tunanin kara dage kidayar karo na ukku. Gwamnati zata bude kokon barar ta saboda neman taimakon kudi da neman taimakon kudi da neman taimakon kudi da za'ai wannan aiki, cikin wadanda zata nemi wannan taimakon harda hukumar majalissar dinkin duniya mai kula da kidaya (census) wato United Nations Population Funds (UNPF).
Gomnatin Nigeria tayi kira ga kamfanoni da masu hannu da shuni dasu taimakawa gwamnati da kudi da sauran abubuwan da ake bukata don samun nasarar yin wannan gagarimin aiki.
Daga karshen, babu wata rana da aka sanya don yin aikin koyon kidaya (training) na Supervisors da Enumerators saboda gwamnatin tarayya (Federal Government of Nigeria) da hukumar kidaya (National Population Commission) na cen tana kokarin yadda zata samu kudi don tabbatar da wannan aiki.
Comments