Rigakafin (Malaria Vaccine): Za'a Fara Rigakafin Malaria A Nigeria
Bayanai daga mujallar Health wanda Same Emmanuel ya ruwaito cewa, hukumar dake bada amincewar magunguna a Nigeria wato "National Agency for Food and Drugs Administration and Control (NAFDAC) ta amince da sabon rigakafin R21 Malaria vaccine wanda kamfanin Serum Institute of India ya kirkiro.
Shugaban NAFDAC (Director General) Prof; Mojisola Adeyeye ya fadi haka ranar Litinin 17th April, 2023 a Abuja.
A wannan dalili ne ake cewa Nigeria ta zamu ta biyu bayan kasar Ghana da ta amince da wamnan sabon rigakafin da aka kirkiro a jami'ar Oxford.
Prof. Adeyeye yace maganin zai iya magance cutar malaria ta kananan yara daga dan wata biyar zuwa wata 36 da haihuwa.
Nigeria na jiran akalla kwayoyin ragakafi 100,000 kyauta (Donation) bada dadewa kafin ya shiga kasuwa sannan za'ayi shiri da hukumar lafiya a matakin farko wato National Primary Health care Development Agency (NPHCDA) dan fara aiwatar da ita.
Adeyeye ya kara da cewa, NAFDAC wajen gudanar da aikin ta akan doka ta amince da wannan allurar rigakafin, NAFDAC Act CAP N1, LFN 2004 ta bada amincewa da rigakafin R21 Malaria (Recombinant Adjuvanted) wanda kamfanin Serum Institute of India pvt, Ltd ya kirkiro.
Shi wannan rigakafin R21 Malaria vaccine anyi shi ne a sterile solution wanda yake kunshe da sarrafaffen protein. Adadin da yake shiga jiki (dose) 0.5ml yana kunshe da R21 Malaria antigen 5 micro gram da matrix- M1 50 micro gram wanda aka shirya shi ruwa-ruwa da zubawa a jijiyoyi.
Shi wannan magani ya nuna zai iya magance cutar Malaria ga yara daga wata 5 zuwa 36 da haihuwa kuma ana ajiyeshi cikin sanyi da yakai 2-8°C (temperature 2-8°C).
Bayanan gwaji na wannan magani an bada shi wajaje biyu da tabbatar da ingancin shi. Hukumomin da suka tabbatar da ingancin shi sun hada da: NAFDAC Advisory Committee bisa tsarin majalissar dinkin duniya, international council for Harmonisation of Technical Requirement for Pharmaceuticals for Human Use Guidelines, European Medicines Agency Guidelines da kuma wani bincike na kimiyya da ake kira (Scientific rigour). Sakamakon da aka samu mai kwarin gwiwa ne.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa kasashen Afrika na da sama da rabin mace-macen Malaria na duniya gaba daya, inda Nigeria (31.3%), Democratic Republic of the Congo (12.6%), United Republic of Tanzania (4.1%) da Niger (3.9%).
Kashi 97% na yan' Nigeria na fama da barazanar Malaria
Comments