Kidaya (Census): An Sanya Sabon Lokacin Yin Training Na Supervisors da Enumerators A Census 2023

A baya sanarwa ta nuna cewa 31st March, 2023 hukumar National Population Commission (NPC) zata fara training jami'anta na wucin gadi wato adhoc staffs, yanzu an samu sauyin lokaci saboda wasu abubuwa masu mahimmanci da suka taso.

Bayan wani taron karawa juna ilimi (Workshop) a kan census na 2023 wanda ya gudana a Golden Tulib Hotel na Port-Harcourt dake jihar Rivers, jami'an NPC sun amince da sabbin ranaku na training din supervisors da enumerators.

NPC tace, ta canza ranakun training daga 31st March, 2023 zuwa 11th April, 2023 a gama 17th April, 2023. Wannan ne kashi na farkon training na supervisors da enumerators.

Sannan LGA level Training on Persons' enumerators zai fara a 25th April, 2023 ya kare 29th April, 2023. Wannan ne kashi na biyu na training din supervisors da enumerators.

Census Night kuma zai wakana a 2nd May, 2023, sannan census din zai wakana ne a tsakanin 3rd May, 2023 zuwa 7th May, 2023.

Bugu da kari, wannan sanarwa an bada ta ne a lokacin taron masu ruwa da tsaki na hukumar NPC wanda shugaban hukumar wato Chairman da Commissioners nashi suka halarta.

Daga karshe hukumar tayi Karin hasken canza lokacin ne saboda kulawa da ayyukan addini dake wakana yanzu haka cikin wannan watan na April wato Ramadan.

Comments

Popular posts from this blog

Civil War: Sudan's Political Turmoil and It's Solution

School problem: School Dropout In Nigerian Secondary Schools & How to Reduce It

Conflict: Science, Religion and Culture