Ganin Watan Shawwal (1444): Yaushe Ne Ranar Sallah, Alhamis ko Juma'ah?
Bayanai da kamfanin jaridar Saudi Gazette ya bayar, yace bincike na kimiyya ya nuna da wuya aga jinjirin watan Shawwal ranar Alhamis 20/04/2023 wanda yayi daidai da 29/09/1444 a kasashen Larabawa da sauran sassan duniya.
A cewar shugaban hukumar dake kula da wannan bincike Engr. Majed Abu Zahra yace rana zata riga wata faduwa a inda rana a Makkah zata fadi a 06:42 pm, wata zai kasance saman rana da tsawon 04 degrees, sannan karkatawar wata (elongation angle) daya raba wata daga rana shi kuma ya kai (05 degrees) da kuma hasken wata wato (illumination is 0.2%).
Bugu da kari, wata kuma zai fadi (Moon Set at 7:06pm) bayan Minti 24 da faduwar rana, a lokacin ne sharadin shiga jinjirin watan Shawwal (Condition for entering month of Shawwal will be fulfilled Astronomically) zai cika.
Abu Zahra ya kara da cewa, ganin jinjirin watan Shawwal (Shawwal Crescent) kuru-kuru ko ta amfani da na'ura (Mornitoring device) ba zai yiwuba sai ta hanya kamera ta musammanr (CCD Camera) saboda karancin hasken jinjirin watan (scant illumination) da kuma karancin lokaci da zaiyi kafin watan ya fadi (short duration above horizon).
Ya kuma kara da cewa ranar Juma'ah April 21 rana zata fadi (sun set) da karfe 06:43 pm, wata kuma zai kasance a daidai altitude (at altitude of 16 degrees) da haske na 2.4% (illumination).
A wannan lokacin kowa zai iya ganin wata kuru-kuru kuma zai fadi karfe 08:05 pm na agogon Makkah, zai kasance away daya da mintuna 22 bayan faduwar rana.
Koya ta kaya dai ranar Juma'ah 20/ 04/2023 ko Asabar 21/04/2023 sune ranakun sallah a kasashe da dama.
Saidai bayanai sun nuna cewa akwai yiwuwar ganin wata a wasu kasashe na Yammacin Afrika. Kasashen sun hada da: Najeriya, Niger, Cameroun, Chad, Ivory Coast, Senegal, Ghana, Burkina Faso da sauransu.
Comments