Aure (Marriage): Lokacin Da Yafi Dacewa Mace Tayi Aure Da Fara Haihuwa A Kimiyyance

Yin aure da fara haihuwar yara wasu shawarwari masu girma, na da mahimmanci kafin yin aure da fara haihuwa, mutum ya tabbatar an shirya. Amma wane lokaci ne wanda yafi dacewa mata suyi aure da haihuwa?

A kimiyyance, akwai wasu abubuwa da ya kamata a kula. Bincike ya nuna mata da suka jira har sai karshe shekarun su na Ashiri (late 20s) ko farkon shekarun su na Talatin (late 30s) sun fi samun damar zaman lafiyar aure akan wadanda akayiwa aure da kananan shekaru (early 20s) saboda mutane wadanda suka makara wajen aure sau dayawa sun fi natsuwa da hankali, sannan suna iya jurewa kalubalen aure dake tasowa. 

Wajen haihuwa kuma, shekaru da suka fi dacewa mace ta haihuwa yana tsakanin shekaru 20 da 35. Mata a wannan lokacin sun fi samun lafiyayyen daukar ciki (healthy pregnancies) da samun lafiyayyun yara (healthy babies). Mata wadanda suka jira har zuwa karshen shekara 30 (late 30s) ko karshen shekaru 40 (late 40s) su haihuwa sun fi samun matsalolin haihuwa wajen daukar ciki da haihuwa sannan da haihuwar yara dake dauke da cututtukan gado (genetic disorder).

Akwai bukatar mu tuna akwai banbance-banbance tsakanin mutane (individual difference), sannan abincin wani gubar wani. Wasu mata na iya zabar yin aure da haihuwa da wuri ko kuma yin aure da haihuwa makare, ba matsala bace!

Mafimahimmancin shine idan mutum na da lafiya kuma yanaso ga kudin daukar kalubalen kudi na rayuwar aure, yana iya aure lokacin daya so.

Daga karshen, a kimiyyance jira har sai karshen shekaru na 20 (late 20s) ko karshen shekaru 30 (late 30s) suyi aure da haihuwar yara shine yafi. Amma ya rage ga kowa ya zabi abunda ya hisshe shi.

Comments

Popular posts from this blog

Civil War: Sudan's Political Turmoil and It's Solution

School problem: School Dropout In Nigerian Secondary Schools & How to Reduce It

Conflict: Science, Religion and Culture