Magani (Traditional Medicine): Tumfafiya da Alfanun Ta Ga Lafiyar Al'umma
Itaciyar Tumfafiya (Calotropis Procera) na da dogon tarihi wajen magance cututtuka (diseases) a cikin al'ummomin duniya baki daya. Muhimmancin ta wajen magance matsalolin rashin lafiya yasa masu magungunan gargajiya (Herbalists) basa son mutane na zuwa inda take dan kada su gano magungunan da take su hana su samun kasuwar magunguna.
Kuma, a haka aka rika tsorata mutane akan wannan itaciyar da cewa tana mu'amala da Aljannu (Evil Spirits) tana biyo mutane a gida da sauran su.
Amma a cikin wannan bayanai zaku karanta yadda take amfanar da lafiyar jikin mutum a fagage daban-daban kamar haka:
1. Furen Tumfafiya na maganin mayu matukar gaske. Duk mai cin furen ta maye bayason irin ruhun su, dan haka mutum ya kubuta daga sharrin su;
2. Ana amfani da ita wajen maganin cizon macizai (anti-snake bite). Anan saiwar ta ce babban mahadi dan maganin cizon macizai. Sai a tuntubi masana dan sanin yadda za'ai hadin a koya;
3. Idan aka turara bawon ta aka hadashi da garin Habbatissaudah kowane lungu da sako na gida, zai taimaka wajen hana manyan Aljanu (Evil Spirits) da mugayen macizai (Evil Snakes);
4. Ruwan ta na maganin ciwukan fata (anti-bacterial) kamar su makero, kuraje da sauran cututtuka na saman fatar jiki;
5. Tana maganin dan banza ko dan kakkare idan aka hada garinta dana lalle aka kumsa wajen ciwon. Sannan wannan na amfani wajen maganin ciwon tsagewar yatsa, cin ruwa da sauran cututtuka (diseases) masu kama dasu;
6. Tana maganin tsutsar ciki idan aka markade furen ta aka tafasa aka zuba Zuma asha;
7. Tana maganin tari kamar su tarin mura, Fuka da Lala idan aka turara bawon ta aka shaki hayakin;
8. Mutanen da Aljanu (Evil Spirits) suka aura idan aka turara saiwar Tumfafiya da Gamji da Habbatussaudah a farjin marar lafiyar da izinin Allah za'a samu lafiya;
9. Tana maganin cizon kare (dog bite) idan aka markade ganyayen ta aka zuba gishiri a tafasa tare sai a wanke inda karen yayi cizon, insha Allah zai hana cutar cizon kare ta kama mutum;
10. Tana maganin mutuwar baren jiki (Paralysis) idan aka hada busasshen bawon ta da kitsen Damo a rika shafawa a wajen da abun ya shafa, insha Allah za'a samu lafiya;
11. Masu fama da ciwon shawara na iya tafasa ganyen ta tare da bawon Ayaba a race ruwan a rika wanna sau biyu a rana za'a samu sauki da izinin Allah;
12. Tana taimakawa wajen rage faduwa ga masu fama da cutar farfadiya idan aka dake saiwar da bawon ta wuri guda;
13. Tana maganin ciwon hakora idan aka turara hayakin ta a cikin baki ko bangaren da abun ya shafa.
Sauran cututtukan da Tumfafiya ke magani sun hada da Kurumta, Ciki, Hanta da sauransu. Sai a matsi kwararru dan samun cikakkiyar shawara da karin bayanai na yadda za'ayi amfani da ita.
Kuyi comment idan kun karanta kuma kunji dadin wannan rubutu a kasa.
Comments