Magani (Medicine): Sirrin Dake Cikin Tafarnuwa Wajen Magance Ciwon Sankara

Dayawan mutane sun yarda cewa Tafarnuwa (Garlic) na da karfin yakar cutar sankara (cancer) saboda sabon bincike na kimiyya da ya tabbatar da cewa tana yakar wasu daga cikin ciwukan sankara (cancer).

Mafiyawa kuma sun aminta da wani binciken dake cewa cin Tafarnuwa (Garlic) na da alaka da rage yaduwar wasu ire-iren cutukan sankara (cancer) kamar su ta ciki (Stomach cancer), kwankwaso (colon cancer), mafitsara (prostate cancer) da ta nono (Breast cancer).

Sinadarin "fibre" dake cikin Tafarnuwa (Garlic) a taimakawa wajen hana yaduwar mafarar sankara (Tumour) da sauran amfanuka.

Bugu da kari, saboda kasantuwar ta na zama maganin sankara (cancer), Tafarnuwa (Garlic) nada wasu amfanuka ga lafiya kamar su: rage kwajewa (anti-inflammation), rage bargo ( anti cholesterol) da karin karfin dakarun jiki (improve immune system).

Kuma, yana da mahimmanci cin Tafarnuwa (Garlic) a cikin abinci, duk da haka bai nuna a rika cin ta ba tsari.

Amfanukan Tafarnuwa sun hada da: 

1. Yakar kwayoyin cuta dake sanya sankara (antioxidant): akwai kwayoyi da ake kira  "free radicals" wadanda me jawo cutar sankara (cancer), Tafarnuwa na yakar wadannan kwayoyi da samar da sinadarin Apoptosis dake hana yaduwar cutar sankara;

2. Tana hana yaduwar hanyoyin jini dake yada cutar sankara (angiogenesis): Tafarnuwa (Garlic) na dauke da sinadaran dake hana kirkira da yaduwar hanyoyin jini dake yada  cutar sankara (cancer), maye gurbin raunin kundin gadon mutum (DNA), da kare cutukan bakteriya (bacteria) dake habaka cutar sankara;

3. Tana maganin cutar gurbatar jini (infection): Tafarnuwa na kunshe da sinadaran dake taimakawa wajen yakar gurbatar jini (infection) wanda hakan zai taimaka wajen hana gina cutar sankara a jikin mutum;

4. Tana rage hauhawar jini (blood pressure): bincike ya nuna tana saukar da takurar hanyoyin jini (circulatory strain), wanda hakanke taimakawa wajen rage ciwon zuciya (Heart diseases) da mutuwar baren jiki (stroke);

5. Tana kara lafiyar kasusuwa: bincike ya nuna cin Tafarnuwa na kara kariya da karfin karfin kasusuwa kuma na taimakawa wajen sanya sinadarin (osteoporosis) mai amfani ga kashi;

6. Tana taimakawa wajen gudu (Athletic): Tafarnuwa na taimakawa masu gudu musamman wadanda ke sana'ar gudu da karfafa masu gwiwa da rage kasawa (exhaustion);

7. Tana maganin cutukan fata: Tafarnuwa nada sinadaran dake yakar fungi da bakteriya (anti-fungi & anti-bacteria) wanda hakan na taimakawa wajen magance matsalolin fata kamar su kwaljewa (inflammation) da kuma cutukan da ake iya dauka na fata (contagious diseases).

Comments

Popular posts from this blog

Subsidy: Tinubu Orders Shettima, governors to Review Salaries and Palliatives

Niger Coup: Reasons Behind the Overthrown of Mohamed Bazoum by Abubakar Haruna

Inflation: Recent Economic Changes in Nigeria