Kayyade Iyali (Family Planning): Yadda Zakuyi Amfani Da Aloe Vera Dan Kacewa Daukar Ciki

Wani bincike na kimiyya da aka wallafa a jaridar Telegraph 2017 ya bada haske ga milliyoyin mata a duniya dake neman magungunan hana daukar ciki (Contraceptive pills) ba tare da bi baya ba (Side effect).

Haka, kamar yadda editan jaridar ta rubuto wato Sarah Knapton tace wani sinadari (Chemical) da aka samu a cikin Aloe Vera da Thunder god Vine (babu sunan shi da Hausa) ya samar da haske wajen samun wannan maganin marar illa.

Sinadaran da wannan tsirrai ke fitarwa na iya samar da maganin wanda bai bukatar sinadaran hormone a ciki ko kuma "molecular condom" wanda ake sha kafin ko bayan jima'i (before & after pills).

A wajen al'adun magungunan gargajiya wato " Folk Medicine tradition" sinadaran aloe vera da thunder god vine dukansu an ruwaito suna kawar da ciki da ba'a bukata (unwanted pregnancy) da kuma samar da abubuwa masu amfanar jiki.

Bugu da kari, masana kimiyya (Scientists) sun fiddo sinadarai biyu "Lupeol" daga aloe vera da "Pristimerin" daga Thunder god vine wadanda bincike a dakin gwaje-gwaje ya tabbatar suna iya hana maniyyi (Sperm) mamaye kwan mace (Ovum).

Idan aka samar da wannan magungunan, zasu kasance magungunan gaggawa (emergency pills) da za'a rika sha kafin ko bayan yin jima'i (before & after sex) a cewar masu bincike.

A cewar wata jagorar bincike na kimiyya Dr. Polina Lishko daga University of California Berkeley tace, saboda wandannan tsirrai na hana maniyyin namiji (Sperm) haduwa da kwan mace (Ovum) a hankali, zai yiwu su zamo magungunan hana daukar ciki na gaggawa (emergency contraceptives) ana masu lakani da "molecular condoms".

Sinadarin Lupeol na samuwa a tsirrai masu yawa kamar su aloe vera, mangwaro da jijiyoyin dandelion.

Man aloe vera (aloe vera gel) a gargajiyance idan aka hadashi da lemun tsami ana amfani dasu a matsayin magungunan kashe maniyyi (spermicidal).

Kuma, Dr. Lishko tace kada mata su tsorata sinadarin aloe vera bai haddasa matsalar rashin haihuwa.

Masu karatu kada ku damu da cin aloe vera dayawa dan maye gurbin ta da magungunan hana haihuwa na yanzu. An gano cewa sinadarin dake cikin aloe vera zai iya sama maganin hana daukar ciki nan gaba.

Wannan bincike ne, idan an samu sahalewar hukumar lahia ta duniya WHO za'a samar dashi dan amfanin al'umma.

Yi comment a kasa idan wannan rubutu ya amfanar daku! Na gode.


Comments

Popular posts from this blog

Civil War: Sudan's Political Turmoil and It's Solution

School problem: School Dropout In Nigerian Secondary Schools & How to Reduce It

Conflict: Science, Religion and Culture