Azumi (Fasting): Muhimmancin Azumi Ga Lafiyar Yan' Adam
Idan aka cire wajibcin azumi ga musulmai a lokacin watan azumin Ramadan mai daraja, azumi kanshi nada amfani marar misali ga lafiyar mutane.
Daga rage kiba zuwa samar da lafiyayyen jini zuwa ga lafiyar zuciya da kuma lafiyar hanyoyin jini, azumi (fasting) ya zama hanya mafi sauki wajen samar da lafiya da hana tsufa da wuri (anti-aging).
Duk da cewa, ba kowa yasan alfanun da azumi yake kawowa jikin dan Adam ba, a nan zamu tsakuro wasu daga cikin su kamar haka:
1. Cire gurbatattun abubuwa daga jiki (Detoxification): rashin cin abinci na lokaci mai tsawo babbar hanya ce ta wanke jiki daga cututtuka da cin abinci ke kawo su (detoxification), kara lafiyar sassan jiki (body organ), wanke bangarorin jiki dake dagargaza abinci (digestive system), habbaka zagayawar jini (blood circulation) da wanke duk wata cuta dake iya cutar da jiki (toxins);
2. Yana maido da son cin abinci da abun sha ( Improve Appetite): tsawon lokaci da ake shafewa ana cin abinci na haifar da matsalar rashin son cin abinci ga mutane (Loosing Appetite). Lokacin da mai azumi yake azumi zai ji kamar zai iya cinye tarin abinci, amma ana shan ruwa saidai ya ci dan kadan ko kuma da zaran mutum yayi azumi zai ji yana sha'awar abincika kala-kala, komi ya gani yana son ci, wannan ya samo asali ne daga uwar hanji saboda daukar lokaci babu komi a ciki, wanda ana kai azumi sai kaga abinci dan kadan zai iya ci;
3. Yana taimakawa wajen saurin narkar da abinci (Improve metabolism): bayan azumi hana kiba; azumi ma na taimakawa zuciya wajen hiddo da sinadarai (Enzymes) dake dagargaza maiko da kitse a maida su abunda ake cema (bile acid) daga nan a maida shi zafin dake taimakawa wajen saurin markada abunda ya Shiva cikin tumbi;
4. Yana taimakawa wake rage kiba (weight loss): rashin cin abinci na tsawon lokacin da babu sukari jikin mutum. Yin haka na lokaci na taimakawa wajen maida halittar mutum ta asali, rage kitse da rage kiba gaba daya;
5. Yana kara garkuwar jiki (Improve Immune System): yin azumi na taimakawa wajen habbaka samar da jini wanda hakan me taimakawa wajen kara garkuwar jiki;
6. Rage Hawan Jini (Reduce Blood Pressure): barin cin abinci a lokacin azumi na nuna rage shan gishiri, idan mutum ya rage shan gishiri ko ya bar shan gishiri, hakan zai kare shi daga hawan mini gaba daya;
7. Yana taimakawa wajen atisaye (Training): dayan kwararru masu gudu (athletes) na amfani da dubarun azumi dan samun nasara wajen cin gasa saboda kona kitse da daidaita jijiyoyi (muscles);
8. Yana taimakawa wajen habbaka lafiyar zuciya (Cardiovascular function): masu azumi na samun lafiyayyar zuciya, rage maiko a jiki (Cholesterol), taimakawa aikin jijiyoyi (muscles) da taimakawa wajen gyara hanyoyin gudanar jini (Blood Circulation);
9. Yana taimakawa lafiyar kwalwa (Improve Mental Health): rage shan sukari, calorie da gishiri na karfafa yadda mutum take kallon abubuwa, Santa kwalwa fahimta da karfafa tunani (Cognitive Function);
10. Yana taimakawa wajen rage sukari cikin jini (Reduce Blood Sugar): a lokacin azumi sukarin glucose na daidaituwa wanda hakan na kara mutum daga ciwon sukari na type 2 diabetes;
11. Yana hana tsufa da wuri (anti-aging): azumi na sanya sake halittar sababbin kwayoyin halittun girma da hana marassa amfani fitowa, hakan na taimakawa wajen samun lafiyayyar fata (improved skin) da hana tsufa da wuri (anti-aging).
Comments