Harkar Tsaro(security): Gwamnatin Zamfara Ta Amince Yan Jahar Su Mallaki Bindiga
Gwamnatin jahar Zamfara dake arewacin Najeriya ta dauki matakin amincewar yan jahar su mallaki bindiga dan kare Kansu daga yan fashin daji da masu satar mutane domin kudin fansa. A wata sanarwa da kwamishinan watsa labarai na jahar Ibrahim Magaji Dosara ya hitar ga manema labarai jiya Laraba yace gwamnatin ta dauki matakin ne saboda yawaitar hare-haren yan bindiga da fashin daji a fadin jahar. Bugudakari, jahar ta dade tana fama da matsalar tsaro wadda ta kassara zamantakewa da kasuwanci a jahar, rayuwa ta zama abunda ta zama, mutane na cikin matukar damuwa dalilin haka yasa dole gwamnati ta amince al'ummar jihar su kare kansu. Tuni gwamnati ta raba fom 500 ga masarautun 19 dake jahar wadanda bukatar mallakar bindigar su kare kansu. Gwamnatin ta kara da cewa zata shige gaba wajen saukakewa mutane wajen mallakar bindiga musamman ga manoma. Gwamnati ta umurci kwamishinan yan sandar jihar ya baiwa dukkan mutanen da suka dace suna bukatar mallakar bindiga su mallaketa domin kare Kansu...