Rashin Zuwa Makaranta: Abubuwan Dake Haddasa Koma Baya Ga Ilimin Yara A Najeriya

A wani sabon rahoto da hukumar raya ilimi da kimiyya da al'adu ta majalisar dinkin duniya wato UNESCO, tace yankin Afrika na kudu da hamadar sahara shine yanki kadai da a duniya yara da basa zuwa makaranta ke kara karuwa.

Hukumar tace kimanin yara miliyan casa'in da takwas (98) ke basa zuwa makaranta a yankin, a Najeriya kuma kimanin miliyan ashirin na yara ke basa zuwa makaranta, shine adadi mafi girma a duniya cikin al'kalumman.

Rahoton yazo duk da matakan da gwamnatoci ke ikirarin suna dauka a Najeriyar domin inganta ilimi a fadin kasar.

Sai dai masana a kan harkokin ilimi a Najeriya na cewa kudaden da ake warewa dan inganta fannin ilimi da gwamnati zatayi amfani dasu wajen zamanantar da ilimin maimakon gine - gine da suka fi maida hankali Kansu da ansamu gagarumin cigaba.

A wata hira da BBC Hausa tayi da kwamishinan ilimi na Jihad Bauchi kuma mai sharhi akan harkar ilimi Dr. Aliyu Tilde yace babban abunda ke hana yara zuwa makaranta a Najeriya shine batun nisa.
Ya kara da cewa kashi 8 cikin 10 na yara dake zuwa makaranta suna shan wahala wajen takawa ko tafiya mai nisa kafin zuwa makaranta.

Dadi da kari, yace irin wannan yanayi ana samun sa a kusan kowane bangare ko mataki na karatu tin daga firamare har zuwa sakandare da jami'a.

Sannan kuma yace, talauci na taka rawa wajen Samar da ilimi, saboda harkokin ilimi na bukatar kudi, dan haka, I dan talauci na karuwa dole a samu yawan yara da basa iya tafiya neman ilimi.

"Akwai kudi a fannin ilimi, sai dai yadda ake kashe dukiyar ko sarrafa ta na sake nakasa ko karya fannin ilimi".

Dr. Tilde yace galibi ana kashe kudin ne a fannin gine - gine maimakon bada fifiko wajen inganta rayuwar malamai, sayen kayan aiki da sauran abubuwan gudanar da ilimi ta fuskar zamani domin samun sauki.

"Akwai shirye - shirye da yawa da za'a iya amfani da su wajen karfafa gwiwar iyaye su tura ya'yansu makaranta".

Dr. Tilde ya bada misali da jihar Bauchi da sauyin da suka kawo wajen ba su nasara har aka samu dalibai da dama da suka samu nasara a jarabawar WAEC.

Sannan ya soki tsarin ciyarwa a makaranta, yace bai taimakawa saboda a galibin yara saboda abinci suke zuwa makaranta bawai karatu ba.

Daga karshe, sharhin masana na cewa akwai bukatar gwamnatoci su sake daura damara Indai sun shirya inganta Samar da ilimin boko a Najeriya, musamman a wannan lokaci da kasar ke cikin matsalolin tsaro da durkushewar ilimi da yajin aikin malaman jami'o'i da kuma rashin inganta albashin malamai. 

Comments

Popular posts from this blog

Civil War: Sudan's Political Turmoil and It's Solution

School problem: School Dropout In Nigerian Secondary Schools & How to Reduce It

Conflict: Science, Religion and Culture