Illar Cin Naman Kaji: Akwai Illa Cin Naman Kaza Tare Da Fata?
Naman kaza nama ne mai farin jini a wajen al'ummomin duniya gaba daya, zai wahala asamu wanda baya cin naman kaza kuma cin ta baida alaka da wani addini ko canfi.
BBC ta ruwaito cewa, a cikin shekarar 2021, hukumar kula da harkokin noma ta majalissar dinkin duniya ta ce mutanen duniya sun ci akalla tan miliyan 133 na tsokar naman kaza.
Cin naman kaza abu ne mai mahimmanci kuma yana dauke da sinadaran protein da vitamin.
Ya na daga cikin amfanin naman kaza kara lafiyar zuciya, sai dai fatar naman kaza na dauke da kitse kashi 32 cikin 100, wannan na dauke da kitse mai nauyin 32 gram inji Maria Dolores Fernandez Pazos wata matashiya masaniyar abinci mai gina jiki a cibiyar CINCAP dake Argentina Kamar yadda BBC ta ruwaito.
Tace daga cikin kitsen akwai marara illa dake inganta awon cholesterol a cikin jini, kuma kashi 3 na kitsen ke da illa kuma yana kara yawan cholesterol marar amfani ga jiki.
Ta kuma bayyana cewa idan mutum yaci naman kaza tare da fatar, yana kara yawan sinadarin calories da kashi 50 cikin 100.
Duk lokacin da mutum ya ci naman kirjin kaza marar fata, zai kara sinadarin calories 284, a cewar hukumar inganta harkokin noma na majalissar dinkin duniya. Kashi 80 cikin 100 na calories daga protein da kashi 20 cikin 100 ne na kitse.
Ma'aunin ya karu duk lokacin da aka hada da fatar idan akaci kirjin kaza da kashi 386 na calories da kuma kashi 50 daga kitse. Wannan dalili ne yasa masaniyar tayi kashedin cin naman kaza da fatar ta da kuma bada shawarar a cire fatar naman kaza kahin a ci, dan kada mutum ya karama abincin shi kitse.
Comments