Tsadar Rayuwa: Hanyoyin Da Zasu Taimaka Maku Rage Kashe Kudi Yayin Hauhawar Farashin Kayayyakin Masarufi
A Najeriya hukumomi sun tabbatar da farashin kayayyaki ya hau da kashi 17.71 zuwa watan Mayun wannan shekara. Haka ya sa rayuwa cikin mawuyacin hali kuma yan kasar na cigaba da fama da tsadar rayuwa.
Haka yasa mutane da dama na tunanin yadda zasuyi da sayen kayayyakin abinci yadda rayuwar ta koma babu kudi a fannin mutane.
Haka zalika, duk da cewa wasu magidanta sun fara matse bakin aljihun su inda suke sayen abunda ya zama dole, amma duk da haka suna so su ga sun rage yan canji a aljihunsu.
A wata tattaunawa da BBC tayi wata kwararriya kan harkokin kudi Oluwatosin Olaseinde wadda ta kirkiro shirin tsumin kudi na "money Africa da Ladda tok".
Masu yada bayanai a intanet sun shedawa BBC yadda za'a rage kashe kudi duba da yadda tattalin arziki ke tafiya kamar haka:
• A sayi abunda ke dole ko ake bukata;
• Babu barna ko amfani da abunda ya wuce bukata;
• A sake duba tsarin jaddawalin abinci ko ayi tsarin " time table" dan tsara yadda za'ayi abinci;
• A sayi kaya tare da mutane da sayen busassun kayan abinci domin ajiye su;
• A tantance kayan dake cikin dakin dafa abinci dan kaucewa sawo kayan da ake dasu;
• Ayi sayayya shago mai rangwame;
• Ayi amfani da na'urorin ajiye abinci kamar firji da kyau;
• A ajiye kayan abinci wajen da bazasu lalace ba;
• Ayi sayayya wajen yan' sari.
Comments