Abinci: Amfanin Cin Kan Kifi

A kasashe da yawa mutane ba sa cin kan kifi, amma a wasu kasashe cin kan Kifi lafiya launae. Abunda dayawan mutane basu sani ba, abu ne mai amfani cin kan kifi. Kada matune su manta shi kan kifi wani 6angare ne na jikin kifin.

Cin kan kifi nada amfanoni biyar ga jikin dan adam. Sune: 

1. Kan Kifi na kunshe da lafiyayyen "protein" sinadari dake sanya kyan fatar jiki da gina jiki a girma. Ba abun 6oyo bane yadda kifi ya zama babbar hanyar samun sinadarin "protein". Naman kifi na rage kamuwa da cututtuka zamani da karancin 6argo marar amfani ga jikin dan adam. Cin naman kifi na taimakawa wajen rage kamuwa da cututtuka masu yawa.

2. Kan kifi na da tarin sinadarin "Omega-3 fat" : da zaran mutum na cin kan kifi zai kara mai yawan wannan sinadarin na "Omega-3 fatty acid" a jiki tunda jikin mutum bai iya samar dashi isasshe, akwai bukatar samaddashi ta hanyar cin kan kifi. Sinadarin "Omega-3 fat" na taimakawa lafiyar kwalwa da hana kamuwa da cututtukan kwalwa.

Wasu bincike-bincike sun nuna sinadarin "Omega-3 fat" na magance matsalar rashin natsuwa, rashin lafiar zuciya, mutuwar 6aren jiki, rage 6argo ko cholesterol daga jiki, hawan jini da rikice - rikice na bugun zuciya.

3. Kan kifi na cike da sunadarin "Vitamin A" : kan kifi na cike da sinadarin "vitamin A", jikin kifin gabadaya cike yake da sinadaran gina jiki. Sinadarin "Vitamin A" na taimakawa garkuwar jiki da yakar abubuwan da ke janyo tsufa da wuri ga fatar jiki, lafiyar ido da rage kamuwa da cututtukan dake haddasa karancin gani.

4. Cin kan kifi na da matukar dadin ci : tarin mai ke dauke cikin kan kifi nada matukar dadin gaske. Naman dake cikin kan Kofi shima yana da matukar dadi. Bayanai sun tabbatar da amfanin cin kan kifi a Africa da kudancin Asia.

5. Cin kan kifi na rage asara :galibin kifaye da kamfanoni ke sarrafawa suna jefar da kawunansu ne cikin shara, hakan na haddasawa muhalli matsala ga 6anna sosai da asarar dunbin dadi. Sannan cin kan kifin zai taimaka wajen karewa da tsaftace muhallin.

Comments

Popular posts from this blog

Civil War: Sudan's Political Turmoil and It's Solution

School problem: School Dropout In Nigerian Secondary Schools & How to Reduce It

Conflict: Science, Religion and Culture