Magani (Traditional medicine 2): Amfanin Gwanda Ga Lafiyar Fatar Mutum
Gwanda na daga cikin kayan marmari masu dadin sha kuma mutane na bukatar ta matuka.
Wani rohoto na Healthline yace shan gwanda wadda take dauke da sinadaran "vitamin A" a ko yaushe na taimakawa lafiyar ido da rashin gani, yakar abubuwan dake sanya tsufa kamar su "Lycopene" da kuma tana cike da sinadaran vitamin C masu yawan gaske.
Bayan gwanda na da amfani wajen ci, tana kuma da amfani idan aka sanya ta a fatar jiki kamar haka:
1• Tana taimakawa wajen goge tsagogi a jikin fuskar mutum da sinadaran dake goge fuska masu taimakawa cire tsagogi da canjin kalar fata. Wani sinadari na beta-carotene da take samarwa na taimakawa fata tayi kyau da kyalli, abunda kawai mutum yake bukata ya narkar da ita bayan cire 6awon sai a sanyata a saman data mai tsage-tsage da canjin kala;
2• Ana sanya ta a fata dan kada ta bushe. Samun lafiyayyar fata na da alaka da shan gwanda sosai, tun da Allah yasa ta na da abubuwan dake yakar tsufan fata, a cire 6awon, na cikin a narkar dashi a zuba na fuska tun da farar safiya, a bata minti 30 sai a wanke a barta ta bushe.
3• Yawan sinadaran carotenoids dake cikin gwanda na taimakawa jiki daga saurin tsufa ta hanyar yakar abubuwa dake sanya tsufa wato "free radicals". Gwanda na taimakawa fata tayi roba-roba da hana duk abunda ka iya sanya ta gautsi. Tana kuma taimakawa fatar diddige idan ana sanya ta sosai a wajen.
4• Ana amfani da ita wajen kare fata daga cututtuka Kamar su eczema, ciwon fata da psoriasis idan aka sanya ta wajen da abun ya shafa ko yaushe. Tana da sinadaran "enzymes" dake taimakawa wajen cire matattar fata.
Comments