Labarai: Ranar Farin Ciki Ta Koma Ta Bakin Ciki, Wata Amarya Da Aka Kama Ranar Daurin Auren Ta

Duk da cewa ranar bikin mutum ranar farin ciki ce, wata amarya a lokacin da ake bikin auren ta yan' sanda suka kamata a Uganda a karshen mako. Ana zargin amaryar da sata da hadin bakin yan' sanda da nuna rashin da'a ga jami'an yan' sanda.

Fred Enanga mai magana da yawun yan' sandan kasar yace idan akasamu jami'anta da laifi a wajen bikin, zasu iya rasa aikinsu.

Da suka kama amaryar sun tafi da ita a ofishinsu dake Mbarara dake Yammacin kasar inda suka tsareta har wanshekare. Sun sake ta ranar Lahadi saboda sunce kamen bai kamata ba kuma rashin adalci ne.

Enanga yace ranar farin ciki a rayuwarta ta koma ta bakin ciki.

Rundunan yan' sandan na tsare da jami'an ta saboda zargin su da hannu a cikin kamen a Cewar Enanga.

Zargin sata da akeyiwa amaryar ya biyo bayan korafe korafe daga tsohon wani abokin aikinta na banki.

Mai magana da yawun yan' sanda yace an basu wata daya su sulhunta kansu.

Sashen bincike na kwararrun yan' sandan na binciken hadin bakin jami'anta hudu da masu korafin.

Sanarwa daga rundunar yan' sandan Uganda tace hakkin jami'anta ne na yin kame da kaiwa kotu, amma hanyar da suka bi bata dace ba.

Jami'an yan' sanda sun baiwa amarya da angonta da yan' uwanta da mahalarta bikin da cocin su hakuri.

Yan' sandan sun bayyana cewa hujjojin da suka tattara sun nuna masu cewa a ranar 6 ga watan Yulin, 2022, wani mai suna Mirembe Henry, tsohon shugaba a tsohon wurin aikin amaryar mai suna Christine Natuhwere da tayi aikin banki, ya kai karar ta satar mashi Shillings miliyan 8.

Yan' sandan sun ce sun binciki lamarin kuma sun tura batun har ga babban alkalin Jihar wanda ya basu shawarar yin sulhu.

Sai dai kuma mai karar ya bukaci a sake duba lamarin da hukunta wadda ake zargi da mayar da karar gaban yan' sanda.

Sanarwar ta kara da cewa a ranar 20 ga Agustan, 2022, jami'an yan' sandan sun hada baki da mai korafi da  tada tarzoma a lokacin bikin auren wadda ake zargi.

Sunyi dirar mikiya a cocin da ake bikin da karfe Takwas na dare dan kama amaryar.

Bayannan, sun sanyata cikin motar mai korafin da kuma tuka motar zuwa ofishinsu, inda suka tsareta can har washegari.

Yan' sandan sun kwatant kamen da akayi a gaban angin da yan' uwa da abokai a matsayi abun kunya kuma bai dace ba.

Comments

Lallae tabbas wannan ranar baqin ciki ce.

Popular posts from this blog

Civil War: Sudan's Political Turmoil and It's Solution

School problem: School Dropout In Nigerian Secondary Schools & How to Reduce It

Conflict: Science, Religion and Culture