Maganin Ciwon Kai (Headache): Yadda Zaku Magance Ciwon Kai Ba Tare Da Shan Magani Ba
Ciwon kai ana iya samun mutum a kowane lokaci, amfi samun shi lokacin tsananin ko idan akwai damuwa ko ansha aiki mai yawa.
Abubuwa da ke kawo ciwon kai suna da yawan gaske, a cewar Dr. Steve kwararren likitan jijiyoyi a (recognitionhealth.com), sun hada da gado, cin abincin jiki baya so, sinadarin jiki (hormones), tsarin rayuwa, canjin yanayi, canjin wuri, gajiya, rashin bacci isasshe, rashin motsa jiki, rashin ruwan jiki da sauran abubuwa da suka shafi lafiya sosai.
A hakikanin gaskia ciwon kai ba ciwo bane kai tsaye, alama ce da ke nuna akwai matsala, jiki na bukatar a kulashi. Galibin mutane sun dauka ciwon kai ciwo ne da ake iya maganin sa kai tsaye, amma abun ba haka yake ba. Zuwa wajen likita kwararren dan tantace mike damunka shine daidai.
Mutane su kaucewa shan magunguna barkatar ba tare da ummarnin likita ba, wani lokaci ma mutum baya bukatar shan komi, amma dole sai likita kwararre ke iya tantancewa.
Ga wasu hanyoyi guda 9 da mutum zai iya magance ciwon kai ba tare da shan magungun ba:
• Shan ruwa mai yawa da zaran mutum yaji kan shi na ciwo, hakan zai taimaka matuka. Idan bai yi ba ana iya gwada na gaba;
• A kula da yawan sukari dake cikin jini, karancin sukari (hypoglycemia) na iya haddasa ciwon kai ga jiki, cewar Deborah ta Dr. Fox online pharmacy (doctorfox.co.uk), matsanancin ciwon kai (migraine) na faruwa ne saboda karancin sukari a jini, idan haka ta faru ga babban mutum yana bukatar shan sukari da yakai 15g da wuri dan magance matsalar ko shan rabin kofin lemun kwalba.
Amma ga wanda yasan yana da ciwon suga (diabetes) to ya matsi likita kahin daukar mataki;
• Yin isasshen bacci na taimakawa wajen magance mafi yawan ciwon kai. An gano mafi yawan ciwukan kai na da alaka da rashin hutu da bacci;
• A kaucewa abincika masu tado ciwon kai Kamar su cakuleti, sukari, naman da ka sarrafa ta zamani, giya, caffeine da cheese Kamar yadda Dr. Leila Dehghan masaniyar abinci mai gina jiki a plant Based Health professionals (plantbasedhealthprofessionals.com);
• Kaucewa amfani da caffeine, sai anyi hankali sosai wajen kaucewa caffeine, yin haka na iya haddasa illar ciwon kai mai tsanani. Kaurace mashi kai tsaye na sanya tuka,kagara da damuwa. Dan haka, i dan za'a kaurace mashi, sai ayi a hankali;
• Kare ido daga matsanancin haske wanda ke sanya matsanancin ciwon kai, ya zama wajibi dan kare kai daga matsanancin ciwon kai a kare shi daga matsanancin haske.
Mutum na iya amfani da gilas, ko rage hasken dake tunkarar ido;
• Kaucewa matsanancin kanshi ko wari na taimakawa wajen rage ko hana ciwon kai Kamar kanshin turare mai karfi kowari ko abinci mai hade - haden ya wuce kima.
A cewar Suzie Sawyer kwararren masanin abinci da lafiya a nature's way (natures-way.com), akwai mutane da yawa da basa son matsanancin kanshi ko wari, idan kuna ciki sai ku kaucewa turare, hayakin taba cigari, abinci mai kanshi sosai, hakan zai taimaka wajen rage samun matsanancin ciwon kai;
• Yin amfani da jikkar kankara wadda ake iya samu sosai a kasuwa na Samar da sauki na wani lokaci a cewar Krishnan. Ana dora ta saman kai dan rage radadin ciwon kai sosai;
• A mai da hankali wajen motsa jiki, dan rashin matsa jiki na da alaka da ciwon kai sosai. Motsa jiki na taimakawa jiki hiddo sinadaran da ke taimakawa rage radadin ciwon kai a cewar Allder, amma kuma, a yawaita shan ruwa wajen motsa jiki musamman lokacin zafi.
Idan matsala ta cigaba a tunkari likita kwararren dan samun taimakon gaggawa.
Comments