Tattalin Arziki: Matakan Da ya Kamata Gwamnatin Najeirya Tabi Domin Magance Matsalar Hauhawar Farashin Kaya
Wani rahoto da BBC ta wallafa ya nuna cewa masana tattalin arziki a Najeriya na fargabar cewa za'a iya samun karuwar wadanda ke fadawa cikin kangin talauci matukar hauhawar farashin kayan masarufi ya cigaba kamar yadda yake faruwa yanzu a cikin kasar.
Rahoton na zuwa ne bayan da hukumar kididdigar kasar tace an samu Karin hauhawar farashin kayan abinci da fiye da kashi ashirin cikin 100 a watan Augusta 2022.
A cewar hukumar wannan ne hauhawar farashi mafi girma da aka samu a Najeriya a cikin shekara 17 da suka wuce.
Dr. Shamsuddeen Mohd masanin tattalin arziki kuma lakcara a jami'ar Bayero ta Kano ya shedawa BBC cewa wasu daga cikin tsare - tsaren da gomnati ta bijiro dasu na taka rawa wajen kara hauhawar farashin kayayyaki a kasar.
Masanin ya bada misali da matakan matse bakin aljihu da gomnati ta dauka a wajen hada - hadar kudade, babban bankin kasa ya kara kudin ruwa sau biyu a jere a watan Yuni da Yuli.
Haka ya kawo dole masu rantar kudade suyi Sana'a zai zama sun samu Karin biyan kudin ruwa wanda zai kaiga tsadar abubuwan da suke sana'antarwa.
Bugu da kari, yace wannan dalili da ya kawo halin da ake ciki, shi ne kara haraji da gomnati tayi kan masana'antu da kasuwanni wanda ya kawo hauhawar farashin kayayyaki.
A cewar Dr. Shamsuddeen, yakin Rasha da Ukraine shima dalili ne mai girma da ya haifar da tashin farashin kayayyaki a duniya gaba daya, Alkama, fetur da dangoginsa da iskar gas sunyi tashin gwauron zabi.
Ya kuma kara da cewa matsalar da za'a iya fuskanta sakamakon hauhawar farashin kayan shine masana'antu zasu iya durkushewa saboda karancin ciniki da rage ma'aikata abunda ka iya shafar tattalin arzikin kasa, yawan talauci zai kari, kullum rashin aikin yi da talauci sai karuwa suke sakamakon hauhawar farashin kaya.
Dr. Shamsuddeen yace matukar gomnati na son taimakawa al'ummarta, toh kamata yayi ta sake nazari kan tsare - tsarenta musamman kan haraji sannan babban bankin kasa shima ya ba da gudunmuwa domin saukaka al'amurra.
Idan gomnati ta kara haraji a lokaci guda bai kamata babban banki ya matse bakin aljihu ta hanyar kara kudin ruwa ba, haka zai shafi tsadar tafiyar da masana'antu wanda zai kara sa farashin ya kara ta6ar6arewa inji Dr. Shamsuddeen.
Bayanan hukumar kididdiga ta Najeriya ta nuna cewar jihar Kwara ce kan gaba da fiye da kashi 30 cikin 100, sai jiyar Ebonyi da Rivers ke bi mata yayin da jigawa da Zamfara da Oyo suka kasance jihohi da ka samu mafi kankantar hauhawar farashin.
Comments