Magani (Traditional Medicine 3): Amfanin Danyar Ayaba (Plantain) Ga Lafiya

Ayaba ko (Plantain) danya ko Ayaba da ake dafawa ko soyawa kamar yadda kowa ya sani, gama garin abinci ne a galibin mutanen yammacin Afrika kamar Najeriya, Camaroon da Ghana. Cikin bayanan zamu mai da hankali wajen amfanin ta ga lafiyar al'umma.

Danyar Ayabar (plantain) ko tsanwar Ayaba na samar da dunbin sinadaran vitamins, minerals, dietary fiber da kuma sinadarai masu yakar cututtuka masu sanya tsufa (antioxidant).

Idan aka cire jin dadi wajen ci, tana da matukar amfani  ga lafiya kamar haka:

1• Tana taimakawa masu ciwon sugar (diabetes) saboda yawab sukarin dake ciki baida yawa idan aka hada da nunnanar Ayabar (Plantain), haka yasa ta zama abinci mai kyau ga masu (diabetes);

2• Tana taimakawa wajen bunkasa sinadarin dake jawo sha'awar jima'i idan ana cinta ko gauche. Sinadaran vitamins da abubuwa masu gina jiki dake ciki suna karfafa karfin yin jima'i;

3• Tana da amfani ga mata masu ciki saboda yaw an vitaminc, calcium, vitamin B-6, phosphorus da magnesium. Duk wadannan sinadaran na taimakawa wajen haiho jariri mai lafiya da gina mashi jiki a cikin ciki;

4• Tana taimakawa wajen magance gembon ciki saboda wani sinadarin da take Samar was wato (Leucocyanidin) wanda ke taimakawa wajen warkar da gembon ciki. Sannan kuma tana taimakawa wajen kare bangayen hanji;

5• Tana taimakawa wajen rage kiba da nauyi, Indai mutum na son rage kiba ya maida hankali wajen cin ta ko yaushe. Tana da abubuwa da yawa dake hana zaman staci a jiki hakan zai sa rage kiba da nauyi;

6• Tana taimakawa wajen hana kumburin ciki, saboda mutane da yawa na gama da wahala kashi saboda dankanoma, dan haka cin ta na taimakawa wajen samun narkewar abinci a samu damar yin kashi ciki sauki;

7• Tana taimakawa wajen gina kasusuwa da hakora masu karfi saboda sinadarin calcium dake ciki wanda ke taimakawa kwarin kasusuwa da karfin hakora;

8• Babbar aminiya ce ga zuciya. Saboda yawan sinadarin pottasium dake ciki wanda take taimakawa zuciya daga hawab mini da matsalar bugun zuciya.

Mutum na iya sarrafa ta a matsayin kunu, ko dafawa da ganyaye da miyar (sauce) ko soyawa da dankalin da sauran su.

Comments

Mashaa Allah. Aeko inshaa Allah Rabbi zan qara dagewa wurin ampani da ita domin samun lpy da kuma gina jikina musamman lpy ta, ta pannin haqora, qasusuwa, da kuma neman kariya daga ciwon sukari (wato) diabetes mellitus.

Popular posts from this blog

Civil War: Sudan's Political Turmoil and It's Solution

School problem: School Dropout In Nigerian Secondary Schools & How to Reduce It

Conflict: Science, Religion and Culture