Kisan Gilla (Murder): An Kama Wata Mata Da Ta Sassaka Gawa Dan Biyan Bashin

Jami'an yan sanda a birnin Yaounde na kasar Kamaru sun kama wata mata a otel dauke da Sassan jikin mutum a cikin akwatin gawa.

Matar mai suna Desire Beyenga an kamata a otel din Mendzang da ke wata unguwa mai suna Biyem-Assi a karamar hukumar Yaounde ta 6 a lokacin da take kokarin Jan babban akwati da ta zuba sassan jikin matar da ake zargi ta kashe.

Dubunta ne ta cika bayan jami'an otel din sun ga alamu na rashin gaskia, bayan bude akwatin sai ga sassan jikin mutum a ciki, haka yasa jami'an Yan' sanda suka tuhumeta.

Desire ta kama daki ita da yar'uwar mijinta Marie Frank Mbeya yar shekara 57, hannuwansu dauke da kwalebanin giya.

A cikin bayanan da tayima jami'an tsaro tace, bayan shigar su daki a otel Jim kadan sai kawai ta buga mata kwalbar giya da soka mata ita. Tace ta aikata hakane saboda dunbin bashin dake kanta har na miliyan hudu, tayi ne dan samun kudin biyan bashin dake kanta.

Ta cigaba da cewa, akwai wani aboki da ta hadu dashi a Facebook bayan komawarsu Yaounde, cikin zantarwarsu take bashi labarin halin da ta Shiga na bashi sai mutumin yayi mata alkawarin bata miliyan biyar idan ta kawo mashi gawar mutum, haka yasa ta aikata wannan laifi.

Yadda akai jami'an otel din suka gano ta ne lokacin da take kokarin hita da babban akwati mai nauyi, ma'aikatan sun shiga zarginta bayan kin ansa tayinsu na daukar mata akwatin, nan ne suka shiga zargin dole sai ambude sunga abunda ke cikin akwatin, da budewa sai suka ga sassan jikin mutum.

Comments

Inna lillahi wa inna ilaehi raji'un!
Allah Ubangigy Ya kawo mamu qarshen wannan lalacewar rayuwa ta qarshen dunia.

Popular posts from this blog

Civil War: Sudan's Political Turmoil and It's Solution

School problem: School Dropout In Nigerian Secondary Schools & How to Reduce It

Conflict: Science, Religion and Culture