Cin kwari: Yadda Cin Fara Ke Amfanar Jikin Mutum
Galibin mutane daga kasashen Yamma cin duniya sun dauka cin fara kazanta ce. Sai dai cin farar nada farin jini a tsakanin mutanen Afirka da Asiya.
Fara na dauke da sinadarai masu mahimmanci da tsafta ga muhalli. Mutane su so ko su ki cin fara ya zama ruwan dare game duniya.
Anyi kiyasin mutum biliyan biyu a fadin duniya ne suke cin kwari a matsayin abinci.
Kwari irinsu fara abinci ce a nahiyar Afirka da Asiya da kuma yankuna tsakiyar nahiyar Afirka. Suna nahiyar Turai sun fara rungumar cin fara.
A wani binciken masana kimiyya sunce cin kwari yana taimakawa matukar gaske wajen gina jiki.
Mutane da dama na cewa kwari na da gishiri - gishiri da kayau-kayau, suna dauke da dandanon magi da daddawa.
Mutane sun rungumi cin fara da kwari saboda suna cin tsirrai, sannan ana samunsu a sassan duniya daban-daban.
Masana na cewa cin kwari abu ne mai dorewa saboda dabbobi na bukatar wajen kiwo da ruwa sosai, su kuma kwari basa bukatar hakan.
Kwari ke Samar mana da kashi 14.5 cikin dari na nau'ukan iska mai dumi da ake bukata a duniyaduk shekara.
Comments