Magani (Traditional Medicine): Tumfafiya da Alfanun Ta Ga Lafiyar Al'umma
Itaciyar Tumfafiya (Calotropis Procera) na da dogon tarihi wajen magance cututtuka (diseases) a cikin al'ummomin duniya baki daya. Muhimmancin ta wajen magance matsalolin rashin lafiya yasa masu magungunan gargajiya (Herbalists) basa son mutane na zuwa inda take dan kada su gano magungunan da take su hana su samun kasuwar magunguna. Kuma, a haka aka rika tsorata mutane akan wannan itaciyar da cewa tana mu'amala da Aljannu (Evil Spirits) tana biyo mutane a gida da sauran su. Amma a cikin wannan bayanai zaku karanta yadda take amfanar da lafiyar jikin mutum a fagage daban-daban kamar haka: 1. Furen Tumfafiya na maganin mayu matukar gaske. Duk mai cin furen ta maye bayason irin ruhun su, dan haka mutum ya kubuta daga sharrin su; 2. Ana amfani da ita wajen maganin cizon macizai (anti-snake bite). Anan saiwar ta ce babban mahadi dan maganin cizon macizai. Sai a tuntubi masana dan sanin yadda za'ai hadin a koya; 3. Idan aka turara bawon ta aka hadashi da garin Habbatissaudah kow...