Furfura (Grey Hair): Dalilan Saurin Fitowar Furfura
Galibin mutane sunyi imani cewa furfura alamace ta tsufa kuma tana fara fitowa mutane yan shekara 50 zuwa sama.
Kash! Saidai akwai mutane kamar ni da furfura ke fitomawa daga shekaru 20. Fitowar furfura da wuri ba alama bace dake nuna wata cuta ta kama mutum ko yaushe, saidai a wasu lokutta.
Babu wani bincike a yanzu dake nuna dalilan da yasa take fitowa da wuri, saidai ga wasu abubuwa dake iya jawo fitowarta da wuri:
1. Shan taba sigari
2. Alepocia areata
3. Yanayin gado
4. Ciwon thyroid
5. Matsananciyar damuwa
6. Amfani da kayan rinin gashi
7. Karancin vit B12, B6, D, E da biotin
Yadda mutum zai rage fitowar furfura da wuri, dubarun hun hada da:
1. Cin kwai
2. Cin Mayan itace
3. Cin ganyaye
4. Shan Madara
5. Shan green tea
6. Cin nama
7. Muamala da man zaitun
8. Cin kifi
Comments