Hakora (Teeth): Yadda Ya Kamata Kuyi Wajen Goge Hakoranku
Goge baki wata al'adace da mutane keyi domin tsafta da kuma kula da lafiyar hakora da bakunansu. Wannan al'ada ta dade tun kafin zuwan man goge baki.
Bayan zuwan Mayan zamani wajen kula da wanke hakoranmu da bakunanmu, bincike ya nuna da yawan mu bamu iya goge bakin ba.
A cewar wani rahoto daga BBC, hukumar inshorar lafiyar ta Burtaniya ta gano cewa kusan Rabin mutum dubu biyu da jami'an lafiyar hakoranta suka tattauna dasu, ba su ma san yadda zasu wanke bakunansu ba yadda ya kamata.
Farfesa Josefine Hirschfeld, kuma kwararriya a fannin lafiyar hakora tace " akwai yiwuwar duk wanda bai tattauna da likitan hakoransa ba yana wanke bakinsa ba daidai ba".
Nigel Carter, wani babban jami'i a gidauniyar lafiya ta oral a Burtaniya shima yace " Ina ganin yana da mutukar rikitarwa yadda ake bada bayanan yadda ya kamata a wanke hakora a intanet ba daidai ba, a haka ake bada bayanan karya".
HANYAR DATA DACE DOMIN WANKE HAKORA
Mafi rinjayen mutane sun dauka cewa wanke baki ko hakora na nufin cire rubabban abinci da ya makale, gaskiyar magana itace bayan cire rubabban abinci da ya makale akwai cire kwayoyin cuta da suke rayuwa a tsakanin hakora da dasashi. Kwayoyin cututtuka da suke yaduwa a wajen sunkai linki 700 daban daban.
Hanya mafi inganci da ya kamata abi domin cire rubabben abinci da kwayoyin cuta a tsakanin hakora da dasashi sune bayan amfani da buroshi sai tura yatsa yana shiga ciki ana goge dasashi da hakoran.
TSAWON LOKACIN DA YA KAMATA A DAUKA
A kwai bukatar daukar a kalla minti biyu ana buroshi da wanke baki da yatsa, wannan sune shawarwari da kunyiyoyin likitocin hakora na Amurka, hukumar lafiyar ta Amurka da kungiyoyin likitocin hakora na Indiya suka bada.
YAUSHE YA KAMATA A WANKE BAKI?
Duk da cewa haryanzu muhawara ake amma likitoci na bada shawarar wanke baki kafin karya kumallo. Saidai am bada shawarar wankewa sau biyu a rana domin hana kwayoyin cuta dake yaduwa a wajen yin tasiri.
Comments