Jima'i (sexual intercourse): Mike kawo Jin Zafi Lokacin Jima'i?

Mutane da dama na kukan jin zafi lokuttan jima'i da iyalensu har matsalar ta jawo rabuwar aururruka masu yawa sosai. Wannan matsalar na hana jin dadin saduwar aure mai gamsarwa sosai da haifar da korafe-korafe tsakanin ma'aurata.

Wannan matsalar ta shafi maza da matansu na aure.

Wai mike kawo wannan matsalar?

Ansa anan itace: 

Abubuwa dake kawo wannan matsalar sun hada da:

1. Tunanin cewa za'a iya jin zafin lokacin jima'in;

2. Matsaloli masu alaka da mahaifa;

3. Ciwon sanyi ga maza;

4. Kumburin prostate ko mafitsara;

5. Sanyin mahaifa ko mafitsara;

6. Yin jima'i bayan haihuwa;

7. Bushewar Mara.

RABE-RABEN JIN ZAFI LOKACIN JIMA'I

1. Akwai jin zafi a farkon al'aura: wannan na faruwa dalilin bushewar gaba ko shigar kwayar cuta;

2. Akwai jin zafi cikin al'ura: wannan yana faruwa ne a dalilin wani aiki na tiyata ko matsalolin mahaifa;

3. Basir: matsalolin basir musamman ga masu shan sukari na haifar da jin zafi a lokacin jima'i, a wani lokacin ma basir din na hana sha'awah gaba daya.

4. Ciwon sanyi ma na sanya al'aurar mace ko namiji radadi lokacin jima'in.

HANYOYIN DA YA KAMATA A BI DAN KAUCEWA WANNAN MATSALA

1. Ga masu matsalar bushewar al'ura, zasu iya amfani da "oestrogen viginal cream" mayukan zamani dan kare al'aura daga bushewa;

2. Idan kuma mai ciki ce ta jinkirta jima'i sai bayan haihuwa da watanni biyu;

3. Idan mace ta kai shekarun barin haihuwa (Menopause) akwai bukatar taga likita;

4. Aje aga likatan jima'i dan samun shawarwari;

5. Idan salon kwanciyar aure ke kawo ta zaku iya canza salon (style).

Comments

Popular posts from this blog

Civil War: Sudan's Political Turmoil and It's Solution

School problem: School Dropout In Nigerian Secondary Schools & How to Reduce It

Conflict: Science, Religion and Culture