Amfani Da Salula (Handsets): Wace Shekara Ya Kamata Yaranku Su Fara Rike Wayar Salula?
A wata hira da BBC tayi da wata kwararraya Dr. Maymunah Kadiri ta bayyana shekarun da ya kamata yaranky su fara rike wayar salula. A cewarta a shekaru na 13 da haihuwa ya kamata yaranku su fara time wayar salula karkashin sa idon iyayensu.
Haka zalika, ta kara da cewa kamata yayi iyaye da makarantu su nemi taimakon kwararru da fasahar zamani wajen sanya ido domin San in halin da yaransu Duke ciki da goge abubuwa marassa amfani.
Kuma, yawanci lokaci yara na kallon abubuwa da suka shafi batsa da abubuwa marassa amfani wanda na iya haifa masu da matsaloli ga lafiyar kwalwarsu.
Dr. Maymunah ta kara da cewa yaran wannan zamanin suna da matukar basira suna son abubuwa da yawa Sannan suna iya tire kowane irin shingle na hanasu Shiva shafukan da bai kamata su shiga ba irinsu Google.
A cewarta yaran na iya nuns bacin ransu akan wannan hanin amma suna bukatar dagiya. Wasu daga cikinsu sunfi shiga shafuka marassa kyau a lokacin suna makaranta "saboda muamala da abokai".
Yana daga cikin bala'in wannan zamani muamala da wayar hannu da shiga intanet ga yara kanana, hakan yaja sun san abubuwan da bai kamata su sani ba sai sun girma.
Comments