Kula Da Iyali: Yadda Zaku Rika Sa Ido Kan Wayoyin Ya'ya'nku

Dr. Maymunah Kadiri wata kwararriya a kan fannin lafiyar kwalwa da gabobi tayima BBC karin bayani akan abubuwan da mutane zasu iyayi dan sanya ido kan yara masu amfani da wayar salula da intanet.

Iyaye na iya sauke manhajar "Family Link" zata bada bayanan shafukan da yara ke shiga da basu kamata ba.

Irin wannan tsarin tabi wajen bibiyar ya'ya'nta dake amfani da yanar gizo.

Sauran shawarwari sun hada da:

• Sanya kariya a talabijin mai tauraron dan Adam Dan toshe tashoshi da bai kamata yara su Shiga ba;

• Sanya kariya a shafikan intanet na iyaye kamarsu YouTube da Netflix;

• Kula da yadda suke amfani da Wi-Fi;

• Hukumomin makarantu da iyaye su rika binciken wayoyin dalibansu musamma  yan makarantun kwana;

• Sanya ido akan abubuwan da yaranku suke musamman cikin dare bayan kowa ya kwanta;

• Amfani da WhatsApp web wajen shiga cikin abubuwan da suke tattaunawa a ciki da sanin suwa suke abota dasu;

Zan rufe da tawa shawarar wadda itace yi masu nasiha akai-akai da tsoratar dasu akan abunda  ka iya cutar dasu wajen amfani da wayarsu da intanet.

Comments

Popular posts from this blog

Civil War: Sudan's Political Turmoil and It's Solution

School problem: School Dropout In Nigerian Secondary Schools & How to Reduce It

Conflict: Science, Religion and Culture