Karin Jini (Blood Tonic): Yadda Zaka Kara Jini Cikin Sauki Da Kanka

Mahimmancin jini a jikin dan Adam ya wuce tunani matuka, domin gudanar da ayyuka na yau da kullum jiki na bukatar wadataccen jini, yana cikin aikin jini zagayawa da abinci cikin jiki bayan maida shi sinadarin da jini ke iya daukar sa.

Sannan jini nada kwayoyin halittu kamar haka:

• Red Blood Cells (Kwayoyin jini jajjaye).

• White Blood Cells (Kwayoyin Jini Farare).

• Plasma (Ruwa mai dauke da abinci).

Ya zama wajibi mutum ya inganta wadatar jini a jiki saboda karancin jini a jiki na haddasa rauni a jiki.

Akwai abinci da dama dake kara yawan jini a jikin dan Adam. Sune ya kamata mutum yaci dan Karin yawan jini.

ABINCI MAI DAUKE DA SINADARAN IRON

Sun hada da kifi, madara, wake, nono, Jan nama, cin anta, cin koda, cin naman kaji, kwai da ganyaye.

ABINCI MAI DAUKE DA SINADARAN FOLIC ACID

Sun hada da alayyahu, ayaba, anta, wake, lemun tsami, lemun zaki da kwai.

ABINCI MAI DAUKE DA SINADARAN VITAMIN C

Sun hada da tumatari, lemun tsami, lemun zaki, Jan nama, naman kaji, kwai da alayyahu.

Idan har jiki na samun wadannan abincikan, jikin zai samu wadataccen jini dan samun kariya daga cututtuka.


Comments

Popular posts from this blog

Civil War: Sudan's Political Turmoil and It's Solution

School problem: School Dropout In Nigerian Secondary Schools & How to Reduce It

Conflict: Science, Religion and Culture