Kula Da Jiki: Dubarun Gyaran Jikin Mata Da Suka Wuce Shekaru 50

Kamar yadda lokacin balaga da kuruciya suke cike da kalubale haka shekarun tsufa suke cike da nasu kalubalen. Mata da suka wuce shekaru hamsin na da bukatar amfani da dubaru domin gyaran jiki sosai dan kare martabar fatar jikinsu da dubarun ingantasu.

Akwai bukatar sanin dubaru domin gyaran jiki ga mata da suka wuce shekaru hamsin wanda ba sai sun kashe kudade ba masu yawa.

<script async src="https://pagead2.googlesyndication.com/pagead/js/adsbygoogle.js?client=ca-pub-6362946090284915"
     crossorigin="anonymous"></script>
<ins class="adsbygoogle"
     style="display:block; text-align:center;"
     data-ad-layout="in-article"
     data-ad-format="fluid"
     data-ad-client="ca-pub-6362946090284915"
     data-ad-slot="7023610059"></ins>
<script>
     (adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
</script>

Wata mujallar kiwon lafiyar bil'adama ta Amurka WebMD, ta tattauna da kwararru a fannin kula da lafiyar fatar jiki da kuma gyaran jikin, sun bayyana dubaru daban daban yadda ya kamata mata da suka wuce shekaru hamsin za suyi domin kula da jikinsu da nagartarsu.

Daukar lokaci cikin rana, shan taba sigari, kula da yanayin abinci, gado suna bayyana sosai lokacin da jikinsu ke kara shekaru kamar yadda mujallar ta WebMD ta nuna.

Kuma mujallar ta nuna tsukewa, Karin nauyi, kiba na matukar shafar jikin mutum, don haka, yayin da mace take sabbin kwayayin halitta cikin hanzari kamar yadda ta saba abaya. Hakan ma na shafar sunadaran launin gashi wanda ke sanya gashi furfura.

DUBARUN GYARAN JIKIN MATAN NAJERIYA SABODA SHEKARU

BBC ta tattauna da wasu Matan da suka haura shekaru hamsin a Najeriya, sun bayyana mata yadda sukeyi domin inganta kyawun jikin fatarsu da sauran jikinsu.

A cewarta Malama Aisha Umar Sani ta kan hada abubuwa kamarsu kurkum (Tumeric) da madara ta kwa6a ta shafewa jikinta kafin shiga wanka ko kuma wani lokaci ta hada ta tasha, sannan tace tana ganin sauyi sosai.

Tace akwai magunguna da mayuka da ake shigowa dasu marassa illa da ake sarrafawa daga ganyaye da saiwoyi da kuma tsirrai.

Hadiza Muhammad ma ta shedawa BBC cewa tana bibiyar masana kiwon lafiyar da gyaran jiki a kafofi daban daban na sada zumunta saidai tace gaskiya saboda tsadar rayuwa mata dama basu samun sukunin Sayan irin magungunan da Malama Aisha ta bayyana.

Ta kara da cewa "na kan samu ganyayen itacen dogon yaro (NEEM) in kir6a shi da kurkum da zuma inrinka shafawa jikina ya dade jikina sai inyi wanka, amma akwai wahala da cin lokaci".

Sauran hanyoyin sun hada da: kin shan taba, kin shiga rana, yin amfani da mayukan kare zafin rana, yawa zuwa wajen likita dan duba fatar jiki domin kare ta daga kansar fata, hana fata bushewa, cin abinci mai kyau da yawan shan ruwa, motsa jiki da gyaran gashi.

Comments

Popular posts from this blog

Civil War: Sudan's Political Turmoil and It's Solution

School problem: School Dropout In Nigerian Secondary Schools & How to Reduce It

Conflict: Science, Religion and Culture