Matakan Tattalin Arziki: Dubarun Rage Cin "Data" Don Shiga Intanet
A yanzu data nada matukar amfani ga rayuwar al'ummar duniya baki daya saboda masayar bayanai. Mahimmancin data a yanzu ya kusa daya dana abinci da kudin kashewa. Amfani da data bai tsaya kan samari da yan'mata ba, kawao harda manyan mutane saboda shiga dan sanin halin da duniya take ciki. Duk duniya anti itifakin Najeriya na daya daga cikin kasashr masu tsadar data, wasu kasashen data kyautane da zaran ka sayi katin buga waya za'a bada data kyauta. Yan' Najeriya sunyi koke-kore kala-kala dan rage farashints amma abun yaci tura. Kamfanonin wayar na koken cewa rashin wutar lantarki da tsadar diesel na sanya sana'ar tasu cikin gararin tsada, shiyasa farashin data da kira ways ya gagara raguwa a kasar. Duk da haka mutum na iya amfani da dubaru dan rage banna da asarar data lokacin shiga yanar gizo ta intanet. Dubarun sun hada da : 1. Iyakance yawan "Data" da manhajojji waya zasuyi amfani dasu wanda a turance ake cewa "data limit". Wannan na daga cik...